
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Doguwa/Tudun-Wada a jihar Kano, Hon. Alhasan Ado Doguwa ya yi alwashin kai jam’iyyar APC ga nasara a zaɓen gwamnan Kano na shekarar 2027.
Doguwa ya faɗi hakan ne a ranar Lahadi a Abuja, a lokacin da ya ke mayar da martani ga takwaransa na mazaɓar Ƙiru/Bebeji, Abdulmumini Jibrin na ce masa (Doguwa) ya zama matsala ga nasarar APC a jihar.
Jibrin ya ce Doguwa nauyin ne ga jam’iyyarsa. Sai dai bai amince da waɗannan kalamai, ya na mai cewa zai tabbatar APC ta yi nasara a babban zaɓen 2027 inda ya ke neman a bashi muƙamin Darakta-Janar na jam’iyyar a jihar.
“Ni ba nauyi ba ne ga siyasa a Kano. Ni kadara ce, kuma abin alfahari ga APC jihar da ma Nijeriya”, inji Doguwa.
Haka kuma Doguwa, shi ne shugaban kwamitin albarkatun man fetur a Majalisar wakilai kuma shi kaɗai ne ɗan APC da ya ci zaɓe a Kano ta Kudu a irin kujerarsa.
