Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A tarihin Nijeriya, an gudanar da jerin zanga-zanga daban-daban waɗanda suka girgiza gwamnatocin ƙasar, wasu daga ciki kuma har suka kusa kawo cikas musamman ga yanayin gudanar da ƙasar.
Akasarin zanga-zangar da ake yi a ƙasar ana yi ne domin adawa da wani tsari na gwamnati ko kuma nuna rashin goyon baya ga wani mataki da gwamnatin ta ɗauka ko kuma ta ke shirin ɗauka.
Wasu daga cikin zanga-zangar sun yi tasiri wajen kawo sauyi, wasu kuma an yi su ne kawai an tashi ‘huhun-ma’ahu’ ba tare da samun sauyi ko kuma cimma burin waɗanda suka fito zanga-zangar ba.
Jaridar Blueprint Manhaja za ta yi dubi dangane da wasu daga cikin zanga-zangar da aka yi da suka girgiza Nijeriya.
1. Zanga-zangar ‘Ali Must Go’ (1978):
Ta farko ita ce zanga-zangar ALI MUST GO, wato DOLE ALI YA TAFI, a shekara 1978, saboda gwamnatin sojin Janar Olusegun Obasanjo ta yi ƙarin kobo 50 a kuɗin abincin ɗalibai daga Naira ɗaya da kobo 50 zuwa Naira biyu.
Wannan ƙarin sule biyar ya sa ɗalibai bore a sassan Nijeriya, irin su Legas, Kaduna, Zariya da birane.
A sakamakon wannan zanga-zanga aka rasa ran ɗalibai 8 a Jamia’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da wani ɗaya daga Jami’ar Legas (UNILAG).
2. Zanga-zangar ‘SAP’ (1989):
Zanga-zangar SAP wadda aka gudanar a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ta girgiza Nijeriya.
ɗimbin ɗaliban jami’a ne suka yi zanga-zangar sakamakon bashin da gwamnatin ta ciyo daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF) a ƙarƙashin shirin SAP domin rage matsalar tattalin arziki.
A lokacin IMF ta shar’anta wa ƙasashe masu karɓar bashin su ɓullo da wasu tsare-tsaren tattalin arziki da suka haɗa da cefanar da kamfanonin gwamnati, zuba jari a ƙasashen waje da sauransu.
An gudanar da zanga-zangar ce sakamakon illar da waɗannan tsare-tsare suka yi a rayuwar ’yan Nijeriya.
3. Zanga-zangar ‘June 12’ (1993):
An gudanar da wannan zanga-zangar ne a zamanin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, a shekarar 1993.
Zanga-zagar June 12 ta ɓarke ne yankin Kudu maso Yamma, bayan gwamnatin Babangida ta soke zaɓen shugaban ƙasa da ake zaton cewa Cif Moshood Abiola ne ya lashe.
Mutane da dama sun rasa rayukansu a sakamakon wannan tarzoma ta June 12.
An yi wa zanga-zangar laƙabi da June 12 ne, kasancewar a ranar 12 ga watan Yunin shekarar aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da aka soke.
3. Zanga-zangar ‘Occupy Nigeria’ (2012):
An fara gudanar da wannan zanga-zangar ne a watan Janairun 2012 a lokacin mulkin PDP, watanni kaɗan bayan an sake rantsar da Shugaba Goodluck Jonathan a matsayin shugaban aasar.
Zanga-zangar ta samo asali ne sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin aasar ta yi inda ɗaruruwan mutane suka fito a manyan garuruwa kamar Abuja da Kano da Kaduna har gaban ofishin jakadancin Nijeriya da ke Ingila.
A lokacin, wasu masu zanga-zangar sun rufe gidajen mai tare da kulle manyan hanyoyi. Hakazalika, manyan ƙungiyoyin awadago na ƙasar sun ayyana shiga yajin aiki har sai an dawo da kuɗin man fetir yadda yake kafin ƙarin da aka yi.
4. Zanga-zangar ‘Bring Back Our Girls’ (2014):
Zanga-zangar BringBackOurGirls ta samo asali bayan da ‘yan ƙunigyar Boko Haram suka sace sama da mata 200 a wata makarantar sakandare da ke Chibok a jihar Borno.
Wannan zanga-zanga ta ja hankalin ƙasashen duniya da shugabanninsu da dama, ciki har da Michelle Obama, matar tsohon shugaban Amurka, sakamakon sace matan masu yawa haka wani abu ne da ba a saba gani ba a duniya.
5. Zanga-zangar ‘Open NASS’:
An gudanar da zanga-zangar OpenNASS domin tabbatar da Majalisar Tarayyar Nijeriya na gudanar da ayyukanta a bayyane ba tare da rufa-rufa ba, da kuma rage kuɗin da suke kashewa a matsayin kasafinsu.
Wasu daga cikin buƙatun masu zanga-zangar sun haɗa da buƙatar majalisar ta bayyana ainahin yadda ta ke kashe duka kuɗaɗen da ta kasafta.
Da kuma aikin majalisar ya zama na wucin gadi domin kawo sauƙi ga irin kuɗin da ake kashewa.
6. Zanga-zangar ‘Not Too Young To Run’:
Wannan zanga-zangar dai ta fara ne a shafukan sada zumunta musamman Tiwita da taken – #NotTooYoungToRun, wanda ƙudiri ne na neman bai wa matasa damar takarar muƙaman siyasa a aasar.
Hanƙoron da matasan ƙasar suka riƙa yi ne yasa wannan ƙudirin har ya kai gaban majalisar tarayyar ƙasar inda a farko aka yi watsi da shi.
Watsi da ƙudirin ya jawo ɗaruruwan matasan ƙasar bazuwa kan titunan domin gabatar da gangamin ƙin amincewa da hakan.
7. Zanga-zangar ‘EndSARS’ (2020):
Wannan zanga-zangar dai ta fara ne tun tuni a shafin Tuwita, inda a duk lokacin da aka samu rikici tsakanin SARS ɗin da wasu ‘yan ƙasar, akan tattauna taken #ENDSARS a shafin Tuwita. Da an tattauna na kwana biyu, sai kuma maganar ta mutu.
Sai dai a baya bayan nan da alama tura ta kai bango, sakamakon zanga-zangar da aka shafe lokaci ana yi a Tuwita ta sa mutane suka fara fitowa kan tituna suna gudanar da zanga-zangar.
8. Zanga-zangar ‘End Bad Governance’ (2024):
Wannan ita ce zanga-zanga ta baya-bayan nan wadda ta fi jan hankali a ƙasar wadda kuma ta nemi girgiza ƙasar.
’Yan Nijeriya na yin zanga-zangar ne kan matsin rayuwa sanadiyyar tashin gwauron-zabi na farashin kayan masarufi, wanda ba a taɓa gani ba a shekarun baya-bayan nan.
Hukumomi sun roƙi masu zanga-zangar da su janye, amma abin ya ci tura. Alhamis, ɗaya ga watan Agusta ne ranar farko ta zanga-zangar wadda aka tsara yin ta a tsawon kwana 10.
Daga baya zanga-zangar ta rikiɗe ta zama tarzoma, inda a wasu biranen ƙasar aka ga masu zanga-zangar suna ɗaga rutur ƙasar Rasha, wanda hakan bai yi wa hukumomin Nijeriya daɗi ba.
