LAFIYA JARI: Fitsarin jini

Spread the love

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

Tabbas fitar jini a cikin fitsari abin damuwa ne ga wanda ya ke yin sa. Wasu lokutan alamu ne da ke nuna cewa, an samu matsala a hanyar fitsari. A wasu lokutan kuwa, hakan na nuni da cewa, an yi amfani da wani abu da ya shiga ya sauya yadda jiki ke gudanar da ayyukansa. Misali, shan wani magani. 

Rabe-raben fitsarin jini:

A kimiyyar likitanci, an raba fitsarin jini kashi-kashi.

1. Akwai wanda ake iya gani da ido ƙuru-ƙuru; akwai kuma wanda sai an leƙa na’urar gwaje-gwaje mai kambama girman abu a idanu, wato “microscope”.

2. Akwai fitsarin jini na gaske, akwai kuma na gangan. Na gasken shi ne wanda ake iya gani da idanu. Na gangan ɗin kuma shi ne wanda ’yan tsirarun ƙwayoyin halittun jan jini suke suɓucewa su shiga hanyar fitsari, amma ba a fiya ganin su da ido ba. Ana samun hakan ne bayan mutum ya yi aikin ƙarfi mai yawa ko kuma ya motsa jiki sosai. 

3. Akwai fitsarin jinin da ke fita da zafi, akwai kuma wanda ba ya fita da zafi. Idan har mutum na yin fitsarin jini wanda ba ya fita da zafi, to hakan abin tsoro ne, domin hakan zai iya kasancewa ciwon daji na mafitsara.

4. Akwai fitsarin jinin da ke fita a lokuta daban-daban na zangon fitsarin. An raba wannan kashi uku: 

a) Jinin ya fara fitowa sai kuma fitsarin ya biyo baya.

b) Jinin ya haɗe da fitsarin su dinga fita a tare. Ko kuma 

c) Jinin ya biyo ƙarshen fitar fitsarin. 

Kowanne da irin abinda yake nunawa. 

5. Akwai fitsarin jini mai zuwa ya tafi, wato idan mutum ya yi shi na ’yan kwanaki, sai ya daina. Sai kuma ya sake dawowa. Akwai kuma wanda yake da naci, ba ya tafiya. Yana nan koda yaushe.

6. Wani fitsarin jinin ya kan yi guda-guda na jini har ma ya toshe hanyar fitar fitsari. Wani kuma jinin ne ba tare da guda ba, za ka ga fitsarin jawur.  

Saboda haka idan ka zo da matsalar fitsarin jini, likita zai yi maka tambayoyi a cikin waɗannan abubuwa da na zayyana, domin a gane a ina matsalar ta ke. 

Sababai:

Abubuwan da suke kawo fitsarin jini su ne:

1. Kansar mafitsara

2. Kansar ƙoda

3. Tsukewar hanyar wucewar fitsari. 

Jin rauni a ƙoda, bututun da ke jawo fitsari zuwa mafitsara ko kuma ita kanta mafitsarar. Raunin zai iya kasancewa ta hanyar haɗarin mota ko na babur ko kuma wani makami. 

Shan wasu maguguna 

Tsargiya 

Tsakuwa a hanyar wucewar fitsari

Tasawar soson da ke tace jini a cikin ƙoda, domin ya samar da fitsari

Shigar ƙwayar cuta ko “infection” kan iya jawo wannan tasawar

Da sauransu. 

Wahalhalu:

Fitsarin jini zai iya kawo wahalhalu da dama irinsu:

Fargaba, ciwon kai, kasala (saboda ƙarancin jini)

Rashin isasshen jini a jiki

Rashin fitar fitsari (idan guda-gudan jini ya toshe hanyar)

Hanyoyi mafi hatsarin kamuwa da fitsarin jini:

Direbobin tanka

Masu shiga ruwa/kogi su yi wanka

Masu aiki a ma’aikatun sarrafa fenti, kayan kwalliya da kayan kashe ƙwarin gona.

Allah ya ba wa jama’a lafiya, amin. Ku tara a rubutu na gaba makon gobe da yardar Allah. 

Naku, MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

By ukarofi