Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya ƙaddamar da motoci ma su amfani da gas

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da rukunin farko na motocin bas da ke amfani da gas (CNG) a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Motocin waɗanda adadinsu ya kai guda 20 ƙirar kamfanin Innoson-built an samar da su ne a Nijeriya.

Gwamnati ta ce motocin zasu taimaka wajen rage wahalhalun sufuri a cikin birnin tarayya, Abuja.

An gabatar da biyar daga cikin motocin zuwa cikin Fadar inda shugaba Tinubu inda ya ɗauki hutu daga zaman Majalisar Zartarwa, FEC domin ƙaddamar da su.

Sauran bayanai za su zo daga baya…..

By Babaji