Daga RABI’U SANUSI
Rundunar ‘yan sadan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin kwaminshinan ‘yan sanda CP Salman Dogo Garba tayi nasarar kama masu laifi daban-daban har mutum 873.
Wannan na zuwa ne a lokacin da rundunar tayi taron baje kolin masu laifuffukan daban-daban a hedikwatar ta.
CP Salman Dogo wanda ya jagoracin gabatar da masu laifin ga manema labarai, yace sun yi amfani da makamar sanin aiki daga jami’an su har akai nasara kamar yadda shugaban rundunar ‘yan sanda ta ƙasa ya basu umarnin aiwatar wa.
Cikin waɗanda aka kama ɗin sun haɗa da mutane 150 da suka ɓarnata kayan gwamnati da dukiyar al’umma yayin zanga-zangar da ta gudana, sai mutane 600 da aka kama da laifin da ya shafi tunzurin zanga-zanga, tada hankali, sace-sace da ɓarnata kayan al’umma da dai sauran su.
Haka kuma rundunar tace ta yi nasarar cika hannu da mutane 6 da ake zargi da kwashe kayan gwamnatin kano tare da ƙonata wanda yanzu haka ana cigaba da gudanar da bincike akan su.
“Mun kuma kama aƙalla mutane da ke ɗaga tutar ƙasar Rasha yayin zanga-zangar har mutum 76 wanda suka haɗa da waɗanda ba ‘yan ƙasar nan ba, da yanzu haka mun tura su babban ofishin mu na Abuja dan a ƙara bincike kan lamarin.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta kuma ƙara nasara wajen kama mutane 41 da laifuffukan fashi da makami, garkuwa da mutane, da satar mota.
Haka kuma sanarwar ta ƙara dacewa ta kama bindiga ƙirar AK-47 guda (2) da sauran kayayyakin da masu zanga-zanga suka ɗauka daga guraren al’umma daban-daban da suka da haɗa da sabon ofishin NCC da babbar kotun Jihar Kano da takardu mallakar gwamnatin jiha.
