Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Kano ta ɗage dokar hana fita daga wannan rana

Spread the love

Daga Rabiu Sanusi

Gwamnatin jihar Kano ta ɗage dokar hana fita sakamakon zanga-zangar da aka yi makon da ya gabata.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a yanzu dai-dai lokacin da ya ke wa manema labarai ƙarin haske bayan duba ɓarnar da masu zanga-zangar suka yi a babbar kotun dake Kano.

Gwamnan ya ce, abin da ya faru ba ɗabi’ar al’ummar Kano ba ce, dan ɗan asalin Kano nada tarbiyyar da ba zai iya aikata wannan aiki ba.

Ya kuma jajenta wa ɗaukacin al’umma da ke aiki a wannan kotun tare da babban Alƙalin jihar, Mai Sharia Dije Aboki.

“Mu na kuma ƙara jajenta wa dukkan waɗanda suka yi asara a wannan lamari da ya faru.”

Haka nan, ya tabbatar da cewa gwamnatin za ta cigaba da bada gudunmuwa wajen ƙara kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kazalika, ya bada tabbacin bada gudummuwa wajen gyare-gyaren wannan kotun da aka ɓata da ƙona motocin ma’aikata.

Sauran bayanai na zuwa…..

By Babaji