Gwamnoni da wasu jiga-jigan APC za su gana don tattauna matsalolin jam’iyyar

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnonin jahohi da Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, Barau I. Jibrin da Kakakin Majalisar wakilai, Hon. Tajuddeen Abbas da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC za su gana a Abuja a ranar Talata don tattauna muhimman abubuwa game da jam’iyyar.

Zaman ya ƙunshi waɗanda ke kan kujerunsu da tsofaffn gwamnoni da sauran masu-ruwa-da-tsaki.

Manyan jam’iyyar a mataki na ƙasa suka shirya taron ƙarƙashin jagorancin zauren samar da cigaba na Ƙasa (NPH) don taya shugaban jam’iyyar da sakatarensa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ajibola Bashiru murnar cikar shekar ɗaya akan muƙamansu.

Farfesa Abiodun Adeniyi daga Jami’ar Baze da ke Abuja zai gabatar da jawabi mai taken ‘Political party Leadership in Nijeriya: Challenges and Prospects’ a Continental Hotel da ke Abuja.

Shugaban jam’iyyar na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje shi ne mai masauƙin baƙi yayin da gwamnoni da wasu manyan jam’iyyar zasu gabatar jawaban fatan alheri.

Kazalika, za a buƙaci shawarwari daga mambobin NPH don bayar da gudumawarsu ga cigaban jam’iyyar a Nijeriya.

By Babaji