
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da gaɓa ta farko ta aikin hanyar Sakkwato-Badagry domin faɗaɗa hanyoyin da zasu sabbaba haɗaka a tsakanin manyan biranen Nijeriya.
Ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Alhaji Mohammed Idris ya faɗi hakan a lokacin ƙaddamar da wani shirin kwana biyu na ma’aikatar da hukumomin da ke ƙarƙashin ta a Abuja.
Hanyar zata haɗe jihohi guda tara wanda haka zai sauƙaƙe harkokin sufuri a tsakanin su.
Baya ga haka, gwamnatin ta ce ta bayar da damar gina madatsun ruwa guda 63 waɗanda zasu taimaka wajen inganta harkokin wutar lantarki da noma a Nijeriya.
Alhaji Idris, ya kuma yi ƙarin haske game da muhimmancin ma’aikatar wajen yaɗa ƙoƙarin gwamnati na ayyukan more rayuwa ƙarƙashin demokraɗiyya ga al’umma, ya na mai cewa akwai buƙatar rassan sanar da al’umma da ɓangarorin ma’aikatar su fahimci cikakken bayanai game da ayyukan gwamnatin.
Bugu da ƙari, ya jaddada aniyarsa ta yin adalci gami da ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da al’ummar ƙasa a yayin gudanar da ayyukan ma’aikatarsa.
