Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A yayin da ake ganin mata marubuta sun ƙwace harkar rubutun adabi, saboda wasu dalilai masu nasaba da samun isasshen lokaci da kasancewar hatta karatun littafin ma yanzu mata ne suka fi yi. Hakan bai sanyaya gwiwar Mustapha Abbas Rijiyar Lemo ba, matashin marubucin da tauraruwarsa ke haskawa a duniyar adabin Hausa, tsakanin maza marubutan onlayin. Kodayake har yanzu yana ganin bugaggen littafi yana da tasiri a wajen masu karatu, ba lallai sai na waya ba. Ya kasance marubucin zube, marubucin wasan kwaikwayo, kuma gwani a harkar ƙawata gine-gine. Wakilin Blueprint Manhaja, ya tattauna da shi kan dalilin da ya sa har yanzu yake cigaba da rubutun adabi, duk da mutuwar kasuwar adabi.
MANHAJA: Ka gabatar mana da kanka.
MUSTAPHA: Sunana Mustapha Abbas Rijiyar Lemo. Ni marubuci ne kuma ɗan kasuwa.
Gaya mana tarihin rayuwarka.
An haife ni a Unguwar Rijiyar Lemo ɗaya daga cikin unguwannin da ke ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano. A nan na yi karatun Islamiyya, da na firamare a wata makaranta da ake kira ‘Yammata Special Primary School. A shekara ta 2004 na shiga ƙaramar sakandire a J.S.S Gogau, daga nan kuma sai na kammala G.S.S Kwachiri duk a Kano.
Gaya mana yadda rayuwarka ta kasance a yayin tasowarka, wanda ya inganta rayuwarka kawo yanzu.
Mahaifana waɗanda suka yi rainona, da tarbiyyata su ne suka inganta rayuwata da ilimina musamman na Muhammadiyya, sannan sun kasance masu ƙarfafa min gwiwa kan duk abinda na sa a gabana na alkhairi.
Yaya aka yi ka fara sha’awar karance-karancen littattafan Hausa?
Ba na mantawa wajejen shekara ta 2000, lokacin muna firamare a bayan makarantarmu akwai kantin sayar da littattafai, a nan nake ganin litattafan Hausa, sai nake jin ya kamata in san mene ne a cikin su, abin na da matuƙar ɗaukar hankali gare ni. Don haka na riƙa tara kuɗin makaranta da ake ba ni har zuwa sa’ar da kuɗin suka kai kimanin Naira 30 a wancan lokacin kuma kusan shi ne farashin littattafan. Ina iya tunawa a irin wannan adashin da nake yi ne na sayi littafin Malikussaifi’ na Aliyu Abubakar Sharfaɗi, da littafin ‘Za Ta Iya’ na Rahma A. Majid. Waɗannan littattafan su ne suka share min hanya zuwa duniyar karatun littattafan Hausa.
Wa ya fara koya maka yadda za ka yi rubutun labari?
Gaskiya ba zan iya cewa ga wanda ya koya min rubutun labari ba, domin daga karatu kawai ni ma na ji ina sha’awar rubutu, don haka na fara. Bana manta yadda na riƙa yi ina yagawa ina sakewa a wancan lokacin. Sai dai daga baya na haɗu da wasu marubutan da suka ƙara saita ni a hanya irin su Nafisat Muhammad Tasi’u marubuciyar littafi ‘Sawun Giwa..
Wanne labari ka fara rubutawa, kuma ko ka fitar da labarin?
Labarin da na fara rubutawa har rubutun ya yi tsayi na kuma kammala shi, shi ne ‘ƙaddarar Mutum…’ har ma kuma na buga shi ya fita kasuwa.
Littattafai nawa ka rubuta kawo yanzu?
Idan ka cire gajerun labarai wato Short Stories, na rubuta littattafai a ƙalla guda 7, sun haɗa da, ‘Halacci Ko Butulci?’ ‘ƙaddarar Mutum,’ ‘Ranar Kuskure,’ ‘Girman Alƙawari,’ ‘Inuwar Sirri,’ akwai kuma ‘Kuɗi Ko Rai’ da ‘So Ko ƙawance?’
Shin ka taɓa buga wani daga cikin labaranka a littafi?
E, na buga guda ɗaya shi ne, ‘ƙaddarar Mutum…’, kamar yadda na faɗa a baya.
Yaya ka ke ji kasancewarka namiji marubuci yadda mata suka ƙwace ragamar harkar rubutun adabi, yanzu ba a cika samun maza sosai ba?
Har yanzu na kasa gamsuwa cewa mata sun ƙwace harkar rubutun adabi gabaɗaya, me yiwuwa ko babu ni a cikin waɗanda aka yi wa ƙwacen. Mata dai sun fi mu yawa a cikin marubuta haka ma a masu karantu, ina ganin hakan na da nasaba da yadda suka fi mu samun isashshen lokacin yin karatu da shi kansa rubutun. Maza kuma sabgogin rayuwa sun musu yawa.
Wanne irin salon labari ka fi jin daɗin rubutawa?
Na fi amfani da salon ɗanmagori ko kuma salon ciki kamar yadda wasu ke faɗa, inda nake barin alƙalamina a hannun tauraro. Kuma labaraina sun fi ƙarfi a ɓangaren zamantakewa.
A cikin masu bibiyar littattafanka, shin ana samun mata da ke neman labaranka su karanta?
Sosai ma kuwa. Zan iya cewa mata su ne kaso mafi rinjaye na masu bibiyar littattafaina.
Wanne abu ne yake ƙara ƙarfafa maka gwiwa wajen cigaba da rubutu?
Masu karatu da bibiyar littattafaina su ne suka fi ƙara min ƙwarin gwiwa, kuma su ne suke sa kodayaushe ba na gajiya da basu abin da suke so.
Shin za ka iya cewa, kwalliya na biyan kuɗin sabulu a rubuce-rubucen da ka ke yi, wajen samun kuɗi daga littattafan da ka ke sayarwa?
Duk da cewa littafi ɗaya na buga kuma a cikin wani yanayi da kasuwar littafi ke fuskantar barazanar durƙushewa, duba da yadda karatun ya koma yanar gizo ni ma na juya akalata inda na saki wasu litattafan nawa a yanar gizon har ma da wanda na buga ɗin ‘ƙaddamar Mutum…’ Sannan zan iya cewa Alhamdulillah, domin kuwa kamar yadda ka ce a tambayar ka, tabbas zan iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Ka san dai yadda harkar rubutu da wallafa take a yanar gizo, tana da sauƙi sosai, ba kamar na wallafa ba, wannan babu wani kashe kuɗi.
Shin kana yin rubutu ne don sha’awa ko don neman kuɗi?
Gaskiya ni ina yin rubutu ne don sha’awa, sai kuma muhimmiyar manufar wato faɗakarwa, tunatarwa gami da nishaɗantar da al’umma. Sannan daga ƙarshe zan iya saka ‘neman kuɗin’, tunda ana nema kuma babu laifi ana samu.
Ta wacce hanya ka ke ganin marubuta za su samu damar cin moriyar ayyukansu?
Ta hanyar ingantawa da tsaftace yadda suke rubutun su, har ma da manufar yin rubutun. Ina nufin kyakkyawar manufa wadda ita ke sawa a ci moriyar ko wanne abu.
Wanne labari ne ya fara fitar da sunanka a duniyar marubuta?
Littafin ‘ƙaddarar Mutum’, sai kuma wasu gajerun labaraina irin su ‘Na Sake Ta’, ‘Laifin Wa?’ ‘Kuɗi Ko Rai’
Shin kana da wani allon kwaikwayo a cikin marubuta, tsakanin mata da maza?
Duk wani tsohon marubuci ko marubuciya allon kwaikwayona ne, domin kuwa har kullum ina jin cewa ba don karatun littattafan baya ba da ba zan zama marubuci ba.
Shin bayan rubutu akwai wata baiwa ta musamman da ka ke da ita, wacce jama’a da dama ba su sani ba?
Ba za a rasa ba. Me yiwuwa a fannin sana’a ta ƙawata gine-gine, da kuma sauran mu’amaloli na rayuwa.
Shin kana rubuta labarin finafinan Hausa, kuma wanne da wanne ka taɓa rubutawa?
E, ina rubutawa sosai. Kuma na juya wasu daga cikin littattafaina irin su ‘Inuwar Sirri’, da ‘Kuɗi Ko Rai?’ Amma ba su fita ba.
Wacce shawara za ka bai wa marubuta maza da suke ƙauracewa rubutun zube na adabi, zuwa rubutun fim?
Idan har suna kishin adabi bai kamata su ƙaurace masa ba, ko da a ce suna samun abinda suke so a harkar rubutun fim. A matsayinsu na waɗanda suka zama tamkar madubi, musamman ga sababbin marubuta masu tasowa. Tsayuwarsu wajen kare martabar rubutun zube na da matuƙar muhimmanci, ko don su ƙarfafa musu gwiwa wanda hakan zai hana harkar ta riƙa samun koma baya. Babu shakka, nasan sun fi ni sani, ubutu al’amari ne mai girma da muhimmanci a cikin kowacce al’umma.
Wanne ƙalubale marubutan finafinan Hausa ke fuskanta daga masu shiryawa?
Wani abokina ya taɓa koka min kan yadda wani mai shirya finafinai wato Producer ya hana shi haƙƙinsa bayan ya sa shi ya rubuta masa fim, daga ƙarshe ma ya daina ɗaga wayarsa. A ganina wannan wani babban ƙalubale ne ga masu rubutun fim, domin ko da a ce ya fi ƙarfin abinda zai ba shi, hakan na iya sawa ya rasa ƙwarin gwiwarsa. Ina nufin zai ji sam ba a mutunta abinda shi yake ɗauka a matsayin sana’a ko wani abu da yake da sha’awa da buri sosai a kai ba.
Shin akwai wasu marubuta mata da ka cirewa hula saboda ƙwarewarsu a harkar rubutu?
Akwai su, suna da yawa har ma ba za su lissafu ba. Kamar irin su, Rahma Abdulmajid, Maimuna Idris Sani Beli, Zainab Kabir Biroman, Sa’adatu Waziri Gombe, Hauwa Lawan Maiturare, Sadiya Garba Yakasai, da Hafsat C. Sodangi da sauransu da dama.
Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarka?
Komai ya yi zafi, maganinsa Allah.
Na gode.
Ni ne da godiya.

