Darakta Janar ta cibiyar cigaban mata ta Maryam Babangida ta sanar da shirin cibiyar na samun haɗin kai da Majalisar Ɗinkin Duniya da Ofishin Jakadancin Kanada domin buɗe wasu cibiyoyin a faɗin ƙasar.
Ta yi wannan jawabin a wani taron ƙarawa juna sani na kwana biyu da a ka shirya ga Kwamishinonin mata na faɗin jihohin Nijeriya 36.
Dakta Asabe Bashir wadda itace Darakta Janar, ta bayyana cewa yin haka zai ƙara wa mata ƙwarin gwiwa domin shiga harkoki a dama da su.
Wakiliyar shugabar mata na Majalisar Ɗinkin Duniya, Zephaniah Aura ta jaddada yadda majalisar ta dage wajen ganin mata sun samu cigaba musamman a Nijeriya.
Ta ƙara da cewa, cibiyoyin nan da za a buɗe, za su zama wuri ne da mata za su haɗu su rinƙa tattaunawa a kan al’amuran da ya shafe su ta ɓangarori da dama misali, shugabanci, sana’a da sauran su. Ta bayyana za a fara buɗe waɗannan cibiyoyin a garin Ekiti, Kwara, Ebonyi da Kaduna.
Jakadan ƙasar Kanada a Nijeriya ya bayyana cewa waɗannan cibiyoyin za su taimaka ƙwarai ganin mata sun samu damammaki musamman a lamuran shugabanci.
A ƙarshe ya bayyana cewa su yi amfani da wannan taron ƙara wa juna sanin domin koyon sabbin abubuwan da za a koyar.
