Atiku ga Akpabio: Ina fatan ba za ku dakatar da Sanata Sumaila ba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Ahugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan tonon sililin da Sanata Abdurrahman Sumaila Kawu ya yi game da adadin kuɗaɗen da sanatoci ke karɓa a matsayin alawus-alawus ɗinsu na wata-wata.

Rahotanni sun ce Sanata Sumaila ya ce, sanatoci na karɓar alawus-alawus na Naira miliyan 21 duk wata baya ga albashin Naira miliyan ɗaya na wata.

Atiku a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ya bayyana iƙirarin Kawu a matsayin jajircewa. Ya kuma bayyana fatan cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ba zai dakatar da Kawu kamar Ningi da Ndume ba.

Wannan martanin na Atiku yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun Paul Ibe, mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, mai taken “Akpabio yana kula da hukumar NASS da ke zagon ƙasa ga RMFAC wajen gyara ma kanta albashi/ alawus-alawus ɗin ta alhali ‘yan Nijeriya na fama da yunwa, talauci, rashin tsaro”.

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce: “Sanata Sumaila Kawu ya yi jajircewa wajen tabbatar da cewa ya koma gida Naira miliyan 21 a kowane wata na alawus-alawus ban da kusan Naira miliyan 1 na albashi don haka ya ƙaryata zargin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo na rashin ɗa’a ga Sanata Godswill Akpabio ta jagoranci NASS ta gyara nasu albashi da alawus wanda ya saɓa wa dokokin Nijeriya.

“Matsayin Sanata Sumaila (Ina fata Sanata Akpabio da ya sare shi ba zai dakatar da shi kamar Ningi ba ko kuma ya tube shi daga mukaminsa kamar Ndume) ba kawai ya tabbatar da abin da Obasanjo ya faɗa ba, yana kuma karya ga martanin da hukuma ta bayar. Majalisar dattijai cewa ba ta gyara nata albashi da alawus alawus. A wata cibiya da ke cike da ’yan wasa da ba su da ƙwallo da za su riƙa yi wa shugaban riƙon sakainar kashi, jajircewar Sanata Sumaila ya cancanci a yaba masa.

Atiku ya ci gaba da cewa, “Amma abin mamaki ne a ce hukumar NASS da ke da alhakin samar da dokoki don gudanar da shugabanci nagari a Nijeriya, ita ce ke karya doka da kuma yin zagon ƙasa ga hukumar tattara kuɗaɗen shiga da kuma kasafin kuɗi (RMFAC), wanda ita ce hukumar da tsarin mulki ya ba wa ikon daidaita albashi da alawus-alawus na jami’an gwamnati, ciki har da mambobin NASS. Haƙƙi ne da ya rataya a wuyan RMFAC ta himmatu da aiwatar da wannan doka dangane da batun daidaita albashi da alawus-alawus na jami’an gwamnati.

“Akpabio da ‘yan ƙungiyar sa na “chop (ping)” yanzu suna iya ganin dalilin da ya sa ‘yan Nijeriya masu fama da yunwa da adalci suka hau kan tituna na tsawon kwanaki 10 a zanga-zangar #EndBack Goɓernance Protest to #EndBadGoɓernanceInNigeria.

“Kuma ga Dele Alakes na wannan duniya, waɗanda (sun) tada injin farfagandar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu: “Motsin” da ya yi ishara da shi ba wai an mayar da hankali ne kan tilasta sauya gwamnati ba, sai don korar yunwa a cikin su. ciki ne ya haifar da manufofin gwaji da kuskure na wannan gwamnati.”

By ukarofi