IPMAN da DAPMAN sun yi fatali da baba-kere a ɓangaren mai

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A daidai lokacin da ake samun takun saƙa tsakanin kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) da matatar man Dangote kan hanyoyin aiki, sauran masu ruwa da tsaki a fannin kamar ƙungiyar Dillalan Man Fetur mai zaman kanta ta Nijeriya (IPMAN) da ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya (DAPMAN), sun yi fatali da masu juya kasuwa, ma’ana ‘Monopoly’ a ɓangaren man fetur.

A cikin jawabai daban-daban da shugabannin ƙungiyar biyu suka gabatar ga kwamitin wucin gadi na majalisar dattijai da ke binciken zargin zagon kasa a fannin man fetur a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata, sun yi gargaɗin cewa cin gashin kai a masana’antar, ba wai kawai zai saɓawa tsarin walwala da aka tanadar ba a shekarar 2021 na Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA), amma zai kawo matsala ga kamfani ko mai saka hannun jari.

Shugaban IPMAN na aasa, Alhaji Abubakar Shettima, ya shaidawa kwamitin da Sanata Opeyemi Bamidele ke jagoranta cewa “Ya kamata a ɗore da tsarin darajar da ake samu a yanzu don baiwa sauran masu zuba jari damar shiga.”

Ya ƙara da cewa, kamfanin na NNPC yana yin iya ƙoƙarinsa amma don Allah a inganta yadda ake samar da kayayyaki zuwa matatu a faɗin ƙasar nan domin kawo ƙarshen layukan da ake yi a gidajen mai.

Da yake bayyana irin wannan ra’ayi, shugaban ƙungiyar ta DAPMAN na aasa, Abdulkabir Adisa Aliyu ya ce son rai yana kashe kasuwanci kuma bai kamata a bar shi a harkar man fetur ba.

A cewarsa, ribar Naira biliyan 133 da aka samu a sayar da sukari a cikin watanni shida na farkon shekarar, wanda Dangote ya bayyana, ya faɗi ne daga hannun jarin da aka amince da shi a harkar.

By ukarofi