EFCC ta bayar da gudunmawar biliyan N50 daga kuɗaɗen da ta ƙwato don tallafa wa ɗalibai

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Masi Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta bayar da gudunmawar zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 50bn domin tallafa wa Asusun Lamunin ɗalibai na Nijeriya (NELFUND).

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Talata, 13 ga watan Agusta, 2024, lokacin da Manajan Daraktan Asusun kuma Babban Jami’in Gudanarwa, Akintunde Sawyerr, ya jagoranci tawagar gudanarwar zuwa ziyarar ban girma a hedikwatar EFCC da ke Abuja.

Sawyerr ya bayyana cewa, asusun, wani shiri na gwamnatin shugaba Bola Tinubu, an tsara shi ne don samar da kuɗaɗe don ilmantar da ɗalibai marasa galihu.

Sanarwar da EFCC ta fitar a wani ɓangare na shafinta na cewa, “Shi Sawyerr ya yaba wa EFCC kan ba da biliyan N50 da aka shigar a cikin NELFUND daga cikin kuɗaɗen da hukumar ta ƙwato.

“Muna sane da kuɗaɗen da aka samu daga wajen masu wawure dukiyar ƙasa, wanda aka miƙa wa NELFUND. Mun zo nan don nuna godiyarmu ga wannan karimcin. Muna kuma son hukumar EFCC ta sanya ido kan abin da muke yi,” inji Sawyerr.

Ya ƙara da cewa “matasan sun kasance mafi yawa a cikin al’umma, inda marasa ilimin mi ke tsunduma kansu cikin tashe-tashen hankula. Shugaba Tinubu ya bayyana hakan a matsayin babbar matsala kuma ya samar da babbar hanyar magance matsalar.”

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya yaba wa Shugaba Tinubu kan wannan shiri, wanda ya bayyana a matsayin “magamce matsalar aikata laifuka

By ukarofi