Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya bayyana cewa an yaudare shi wajen bayar da mallakin fagen kasuwanci ga mayaudaran ‘yan China masu zuba hannun jari.
Amosu wanda ya kasance gwamnan Ogun daga 2011 zuwa 2019, ya fitar da wata sanarwa inda ya ke bayyana cewa tabbas bai yi zurfin bincike ba wajen miƙawa kamfanin ‘yan China mallakin “Ogun-Guadong Free Trade Zone” waɗanda yanzu ke neman kwace kadarorin gwamnatin Nijeriya a ƙasashen yamma da Amurka.
Amosun ya ƙara da cewa, “Ogun Free Trade Zone” gwamnatin bayan shi ce ta fara assasa wannan aiki inda shi ma ya gada. Bayan hawan shi mulki ba da jimawa ba, sai wannan kamfanin na Zhongfu International Investment ya shigo masa da neman a basu wannan wuri su cigaba da kula da shi saboda waɗanda abun ke hannun su yanzu, wato China Africa Investment.
Bayan dogon bincike da gwamnatin shi tayi, ta gano Kamfanin China Africa su ne su ka dace da wannan wuri. Don haka yayi kira ga gwamnatin tarayya da kar ta shiga wani tattaunawa da wannan kamfani na Zhongfu International Investment domin haramtaccen kamfani ne.
