Gwamnan Kano ya bada umarnin yin bincike kan zargin kwangilar magunguna

Spread the love

Daga USMAN KAROFI NASIR a Abuja

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin yin binciken a kan batun zargin bada kwangilar magunguna ga ƙananan hukumomi 44 da ke jihar.

Gwamnan ya nuna rashin sani a kan wannan al’amari don haka ya umarci shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar, Barr Muhuyi Magaji ya gudanar da binciken gaggawa a kan lamarin.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da kwamishinan labarai Baba Halilu Ɗantiye da kuma mai ba gwamnan shwara a harkokin labarai Sanusi Bature Dawakin Tofa su ka sanyawa hannu, ta na cewa an umarci hukumar ta yi gaggawar kai rahoton binciken gaban gwamnan.

Gwamnan ya umarci ƴan jihar da su yi hakuri su saurari rahoton binciken da za a gudanar domin ɗaukar mataki.

By ukarofi