Dillalin filaye ya zargi lauyoyinsa da rashin iya aiki

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Wani dillalin filaye daga Jihar Kebbi mazaunin Babban Birnin tarayya Abuja, Alhaji Ibrahim Mohammed Kamba, ya zargi wasu lauyoyin da ke gudanar da shari’o’insa a kan rashin iya gudanar da aiki cikin ɗa’a.

Kamba, ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce lauyoyin sun haɗa baki da wasu mutane domin su yi masa maguɗi.

Ya bayyana cewa wasu filaye da lauyoyinsa ke gudanar da ayyukansu a babban birnin tarayya Abuja sun haɗa da; Niger Dock Global inɓestment limited with Plot No. 247 Idu 1, Godiya Ga Allah Enterprises with Plot No. 256 Utako, Kamut Enterprises Farms Serɓices dake Central Area, Kamba Inɓestment Nigeria Limited mai lamba 1187 Sector Center D, Kamba Engineering Serɓices da fili mai lamba 1750 Dape, Kosun Chemical Company Limited mai lamba Plot No. 4 Sabo Gida and National Youth Council of Nigeria with Plot No. 523 Kukwaba.

Daga nan sai ya yi kira ga ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) da ta ga ya dace a binciki ayyukan jiga-jigan shari’a kan rashin ɗa’a ga abokan hulɗarsu.

Kamba, ya ce ana kan shirin fallasa wasu lauyoyinsa ga hukumar NBA kan rashin ɗa’a da suka yi.

By ukarofi