Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da buɗe babban asibitin Ƙauran Namoda

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A ranar Talata ne gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da buɗe babban asibiti mai cike da kayayyakin aiki na zamani da aka yi wa kwaskwarima a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar.

Asibitin zai zama wajen karɓar kiwon lafiya ga al’ummar Ƙauran Namoda da maƙoftan garuruwa wanda aka sanya wa kayan aiki don tabbatar ingantaccen kulawa gare su.

Cikin Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamnan ya ce asibitin ya ƙunshi kayan awo, gadon haihuwa, na’urorin ECG, na’urorin tace jini, na’urar gwada nauyi, fitilar aikin tiyata da sauransu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ire-iren asibitin su na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen bayar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar jihar wanda kuma za su ke samu a sauƙaƙe.

A lokacin ƙaddamarwar, Dauda Lawal ya ƙara jaddada aniyarsa ta bada muhimmanci ga ƙoƙarin gwamnatinsa wajen bunkasa ababen more rayuwa da kuma warware matsalolin tattalin arziƙi a kowane ɓangare na jihar.

Sannan kuma, ya ce daga watanni 14 baya zuwa yanzu, gwamnatinsa ta yi gagarumin hoɓɓasa wajen gyara da kuma inganta asibitoci manya (GHs) da ƙanana (PHCs) a sassa daban-daban na faɗin jihar.

Bugu da ƙari, ya ce sun shirya ɗauka gami da horar da malaman harkar lafiya, samar da magungunan da ake buƙata da kuma samar da tsarin karɓar kulawa na ƙanan yara da mata a kyauta.

By Babaji