Za a fara gasar wasan ƙwallon Dawaki a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.

Kamar yadda shugaban ƙungiyar wasan ƙwallon Dawaki a jihar Katsina Alhaji Sanusi Kabir Usman ya faɗawa manema labarai a Katsina ƙungiyoyi guda 33 zasu shiga cikin gasar.

Ya ce jihohi da suka haɗa da Jihar Legas,Oyo, Rivers, Plateau, Kaduna, Kano duk sun nuna sha’awar su ta shiga gasar.

Ya kuma bayyana cewa bana babban kofin na Nigeria cup da yau ya cika shekara ɗari da fara fafatawa shine ƙungiyoyin zasu fafata akai

Alhaji Sanusi Kabir ya bayyana cewa akwai yan wasa musamman daga ƙasar Jamus da sukai rajistar shiga fafatawar cin kofin Nigeria cup dama kofin General Hassan Usman cup.

Ya tabbatar wa ‘yan wasan da samar masu wadataccen masauki musamman ‘yan wasan ƙasar Jamus.

Haka kuma shugaban ƙungiyar ya bada tabbacin tsaro ga ɗaukacin baƙin da za su zo da harda ma su sha’awar kallon wasan da zai ɗauki tsawon mako guda a nayi

Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman shine shugaban ƙungiyar ƙwallon Dawaki ta ƙasa

By ukarofi