Wata ƙungiyar da ake kira ‘Apostles of Jagaban’ sun zargi gwamnoni daga jam’iyyun hamayya da rashin raba tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa a jihohin su.
Shugaban ƙungiyar, Cif Gilbert Olukususi a wata sanarwa da ya bayar ya zargi gwamnonin da karkatar da ta tallafin shinkafa da gwamnatin tarayya ta bayar domin a rabawa a al’ummar su.
Shugaban ya zargi gwamnonin da rashin yin hakan, shi ya ƙara tunzura zanga-zangar matsin rayuwa da a ka gudanar a faɗin ƙasar.
Ya ƙara da cewa, da irin wannan zanga-zangar su ka fake ɓatagari su ka shiga domin har su ka lalata dukiyoyin gwamnati da na al’umma.
