Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta cafke mutane biyar waɗanda a ke zargi a badaƙalar kwangilar magani. Waɗanda a ka kama sun haɗa da Alhaji Muhammad Kabara , Sakataren Dindindin na Ma’aikatar ƙananan hukumomi da sarautar gargajiya.
Akwai kuma, Alhaji Bashir Abdullahi, shine Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin ta Nijeriya, shugaban ƙaramar hukumar Tarauni wanda jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ya tabbatar.
Akwai shima Shugaban kamfanin Novomed Pharmaceuticals, Garba Kwankwaso, wanda ɗan uwa ne ga jagoran jami’iyyar NNPP na ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.
Waɗanda a ke zargin, a na tuhumar su da haɗa baki wajen ba kamfanin Novomed kwangilar kawo magunguna ga ƙananan hukumomi 38, wanda yin hakan ya saɓa wa dokar kwangila ta ƙasa.
Bincike ya nuna cewa kowacce ƙaramar hukuma ta biya naira miliyan 9.15 ga Novomed domin kawo magungunan wanda har yanzu ba a kai su ba.
Hukumar na cigana da zurfafa bincike domin gano irin ɓarnar da aka yi da kuma cigaba da zaƙulo waɗanda su ke da hannu cikin wannan almundahana.
