Shin kashe Haniyeh ya murƙushe Hamas?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Jagorancin ƙungiyar Hamas mai mulkin Zirin Gaza tamkar sayen likkafani ne don kar a wahalar da dangi lulluɓe mutum da zarar an kashe shi. A wasu kalmomin jagorancin Hamas sayan mutuwa ne ko kisa a kowane lokaci masu mamayar ƙasar Falastinawa ka iya aiwatarwa. Mu tuna da yadda jirgin yaƙin Isra’ila ya kai farmaki kan marigayi shugaban Hamas Ahmad Yassin a 2004 ya na kan keken guragu yayin dawowa daga sallar asuba. Haka bom ya kashe shi da masu rakiyar sa. Kazalika shi  ma tsohon shugaban Hamas Abdul’aziz Rantisi haka jirgin yaƙin Isra’ila ya kai ma sa hari ya samu munanan raunuka da su ka yi sanadiyyar mutuwar sa a asibiti. 

Kisan gilla ga manyan jagororin Hamas biyu ya afku ne tsakanin wata Maris da Afrilu na 2004 kuma a kwanaki kasa da wata ɗaya daga harin sojan Isra’ila. Haƙiƙa Hamas ta girgiza a tsakanin nan. Hatta shi kan sa marigayi shugaban Hamas da a ka kashe kwanan nan a Tehran babban birnin Iran ya sha tsallake rijiya da baya. Akwai lokacin da a ka ba da rahoton wani makami mai linzami da a ka harba saitin kujerar sa a ofishin sa a Gaza inda a lokacin Allah ya sa ba ya kan kujerar. Da alamun mutuwa ko kisa ba ya karya gadon bayan Hamas don ƙungiyar ba ta zama ba shugabanci duk rintsi kuma ba ta taba kasa a gwiwa kan neman ’yancin Falasdinawa. Indai  ka ga a kan mutum ɗaya Isra’ila za ta iya tashin jiragen yaƙi don kashe shi amma hakan ba zai sa ya girgiza ko zama a cikin fargaba ba, akwai abun dubawa ga irin wannan jarumtakar ta mutanen nan. 

Hakanan uwaye mata kan gode wa Allah maimakon ɓarkewa da kukan na mutu na lalace a lokacin da a ka kashe ’ya’yan su.  Na lura Falastinawa na girmama wanda ya sadaukar da rayuwar sa kan gwagwarmayar kwatar haƙƙin ƙasar sa a tsakanin su. Tun fa 1948 Falastinawa ke fuskantar hare-hare da barazana kan rayuwar su. A yanzu haka akwai dubban Falastinawa da ke kulle a gidajen yarin Isra’ila. A kan samu matasa da dattawa cikin wadanda Isra’ila kan cafke ta jefa gidan yari. Akasarin dalilan kama Falasdinawa na da nasaba da tsayin daka kan hana Isra’ila cigaba da mamaye ƙasar Falastinawa. Wani lokacin a ka iya cewa gara ma waɗanda a kan jefa gidan yarin a yanke mu su shekaru da dama da waɗanda jami’an tsaron Isra’ila kan harbe a kan titi don zaton su na da hatsari ko su na barazana ga tsaron Isra’ila. Har yau ba a bi kadun jinin Bafalasdiniya ‘yar jarida Shireen Abu Akleh da jami’an tsaron Isra’ila su ka bindige da gangan duk da ta na sanye da riga da ke ɗauke da alamu ƙarara na cewa ‘yar jarida ce. 

Kuma don ma ta na aiki da babbar kafa irin Aljazeera ne ma ya sa maganar ta ɗan yi tasiri kamar za a ɗora wa Isra’ila laifi amma can sai shiru kawai a ke ji wacce ta mutu ta mutu kamar yanda sauran ‘yan uwan ta da a kan kashe su kan zama ba a ma ko ba da labarin muruwar su. Bai ma zama wani abun a yi juyayi ba don an ce an kashe Falastinawa kaza tun da an saba da jin hakan tsawon shekaru gommai da su ka wuce. Wallahi da sauri na kan rufe faya-fayan bidiyo da ke nuna yara ƙanana Falastinawa da hare-haren Isra’ila su ka kashe ko su ka raunata cikin jini. A tsarin yaƙi ba a kashe yara ko mata haka kurum. Ba lallai ne matashin Bafalasdine ya girma har ya zama dattijo ba don a kullum za a iya kashe shi. Da dai duniya na da adalci ba za a riƙa kashe ƙananan yara Falasdinawa ba tare da ɗaukar matakin dakatar da hakan ba. 

Gaskiya kamar ƙudurorin Majalisar ɗinkin Duniya da su ka shafi kare Falastinawa ba sa aiki. Isra’ila na da daga ƙasashe ƙalilan a duniya da kan yi abun da ta ga dama ta kwana lafiya. Kotun duniya ma ta sha takawa Isra’ila birki amma ina sai gwamnatin ƙasar ta yi biris da hukuncin kuma hakan ba ya sa ka ji an ayyana neman kama shugabannin na Isra’ila.

ƙungiyar mayakan Hamas mai mulkin Gaza ta naɗa Yahaya Sinwar a matsayin sabon jagora don maye gurbin Isma’il Haniyeh da a ka ɗora alhakin yi ma sa kisan gilla kan Isra’ila a Tehran.

Sinwar babban jigon Hamas ne kuma shi ya shirya harin da Hamas ɗin ta ƙaddamar a cikin Isra’ila a Oktobar bara da ya haddasa yaƙin da a ke ciki har yanzu.

Wani abun dubawa kan Yahya Sinwar ya na zaune ne a Gaza duk da yanda Isra’ila ta sanya shi a jerin waɗanda ta ke marmarin kashewa.

Sinwar na aiki da babban kwamandan sashen sojan Hamas Muhammad Deif a rundunar aiki da cikawa ta ƙassam.

Isra’ila na cikin shirin ko-ta-kwana don fargabar ramuwar gaiya daga Iran da magoya bayan ta.

Wannan ya biyo bayan harin da a ka ɗora alhaki kan Isra’ila da ya kashe kwamndan Hezbollah a Lebanon Shukr da kuma babban jagoran Hamas Isma’il Haniyeh.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyanawa majalisar sa wannan hali da shiri da Isra’ilar ke ciki.

Amurka da kawayen ta na shirin kare Isra’ila daga duk wani farmaki inda tuni Amurka ta tura ƙarin kayan aiki don taimakon Isra’ila.

A na cikin wannan yanayi Isra’ila ta kai mummunan hari kan wani sansanin gudun hijira a wata makaranta a Gaza inda ta kashe kimanin mutum 100.

Rahotanni daga rundunar Sibil Difens sun ƙara da cewa cikin mutanen da su ka mutu akwai yara 11 da mata 6.

ƙasashe masu tausayawa Falasdinawa sun yi Allah wadai da wannan hari da ya shafi waɗanda ba su yi wa kowa laifi ba.

Zuwa yanzu hare-haren Isra’ila kan Gaza sun yi sanadiyyar mutuwar fiye da Falastinawa 40,000 akasarin su mata da ƙananan yara.

Hakanan Falasdinawa 92,000 sun samu raunuka daban-daban daga hare-haren da su ka haɗa da na ruwan boma-bomai daga jiragen yaƙi.

Ofishin firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da cewa Isra’ilar ta amince ta koma teburin tattaunawa don batun tsagaita wuta a yakin Gaza.

Kamar yadda mu ke nanatawa wannan yaƙin dai da ya faro daga Oktobar bara ya yi sanadiyyar kashe dubban Falasdinawa musamman mata da ƙananan yara.

Masu shiga tsakani da su ka haɗa da Katar da Masar su ka buƙaci dawo da tattaunawar.

Iran ta zargi Isra’ila da neman faɗaɗa yakin ya shafi yankin gabar ta tsakiya gaba ɗaya.

Naɗa Yahya Sinwar ya maye gurbin jagoran Hamas Isma’il Haniyeh da a ka ɗora alhakin kisan gillar sa kan Isra’ila ya nuna fara farfaɗowar Hamas daga juyayin rashin babban jigon ta.

Falastinawa na ficewa daga garin Khan Younis na kudancin Gaza don gujewa  hare-haren Isra’ila.

Wannan na faruwa daidai lokacin da Isra’ila ke gargaɗin Falasdinawa su fice don ta na shirin gagarumin hari.

Kazalika kamar yadda mu ka bayyana hakan ma ya biyo bayan wani mummunan hari da Isra’ila ta kai a yankin na Gaza ta kashe kimanin Falastinawa 100 a wata makarnta da ke ɗauke da ‘yan gudun hijira.

Haƙiƙa Falasdinawa sun shiga yanayin mawuyacin hali a Gaza ta hanyar hijira wa imma daga arewaci zuwa kudanci ko daga kudanci zuwa arwaci.

ƙungiyar Hamas mai mulkin Gaza na bukatar a tafi kai tsaye a yi aiki da shirin tsagaita wuta da shugaban Amurka Joe Biden ya kawo maimakon kewaye-kewaye.

Wannann na zuwa ne daf da ranar da a ke shirin dawowa zaman sulhun da masu shiga tsakani wato ƙasar Katar da Masar ke jagoranta.

In za a tuna Isra’ila ta amince da dawowa kan teburin shawari duk da cigaba da buɗe wuta da ta ke yi da zummar murƙushe Hamas ɗin gaba daya.

Wato dai a nan Hamas na son a tafi kai tsaye wajen amfani da yarjejeniyar ta Biden da za ta kai ga dakatar da yaƙin na Gaza gaba ɗaya maimakon a tsaya cecekuce kamar yadda ya sha faruwa a baya.

A ɓangaren nuna takaici Saudiyya ta nuna damuwa da ya kai ga Allah wadai da maimaita keta haddin masallacin Al-Aƙsa da ke gabashin birnin Kudus da Isra’ila ke yi.

Martanin na Saudiyya ya zo ne bayan ministan tsaron Isra’ila mai tsaurin ra’ayin addinin Yahudanci Itamar Ben Gɓir ya jagoranci daruruwan Yahudawa su ka shiga masallacin su ka gudanar da ibadar Yahudawa da ke alamta fara hutun Yahudu.

Ben Gɓir ya sha keta alfarmar masallacin a baya ta hanyar jagorantar tawaga ya auka  masallacin da hakan ke kawo suka daga Musulmi.

Saudiyya ta buƙaci jan kunnen Isra’ila don ta daina keta dokokin duniya da ma na gwamnatin ta Isra’ila da ta hana ibadar Yahudawa a masallacin.

Kammalawa;

Yanzu za a ƙara zuba ido a ga ko sabon yunƙurin tsagaita wuta a yakin Gaza zai yi nasara ko kuwa a’a tun da Isra’ila ta yi ramuwa iya son ran ta daga harin Hamas a Oktobar bara. Ga shi cikin waɗanda a ke aza alhakin kashe su daga Isra’ila har da shi kan sa shugaban Hamas Isma’il Haniyeh kuma wani abun dubawa da nazari a babban birnin Iran wato Tehran.

By ukarofi