Ƴan bindiga sun buƙaci a ba su N50m bayan yin garkuwa da mutane 10 a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƴan bindiga sun kai hari a garin Moriki da ke jihar Zamfara a ranar Laraba inda su ka yi garkuwa da mutane 10 tare da neman a biya su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.

Wani mazaunin yankin ya ce ƴan bindigar sun addabi garin yayin da a baya ma sun yi garkuwa da wasu mutane a yankin inda ƴan bindigar suka yi ikirarin cewa Kwamandan Moriki ya kashe mu su dabbobinsu.

Ya ce, yau ce ranar ƙarshe da ƴan bindigar suka bayar na lokacin karɓar kuɗin.

Sannan kuma duk sanda ƴan ta’addar ke buƙatar kuɗi, sai su kai hari garin tare da yin garkuwa da mutane har sai an kai mu su kuɗi sannan su sako su.

Ya ƙara da cewa, ba da daɗewa ba suka karɓi Naira miliyan 20 daga mambobin garin don su bar mutanen su yi aiki a gonakinsu cikin lumana.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Yazid Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya na mai cewa kwamishinansu ya umarci a shirya ceto mutanen.

By Babaji