Kwantiragin Damfara: An sako ɗa ga Kwankwaso yayin da kantomomi uku da wasu ke tsare

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar kula da hana rashawa ta jihar Kano, PCACC ta tsare shugabannin ƙananan hukumomi uku na jihar kan zargin badaƙalar Naira miliyan 660 ƙudin ƙwantiragin aikin ruwa.

A ranar Alhamis da misalin ƙarfe 9 na dare ne hukumar ta sako Garba Musa Kwankwaso wanda ɗa ne ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bayan belin sa da aka yi.

Rahotanni sun ce hukumar ta buƙaci ya dawo ofishinta ranar Litinin domin cigaba da gudanar da bincike.

Kantomomi ukun da aka tsare sun amsa laifukan sauya akalan wasu kuɗaɗe zuwa asusunsu na kai-da-kai.

Mutane ukun sune Abdul’aziz Sulaiman na ƙaramar hukumar Ƙiru, Basiru Abubakar na Bebeji da kuma Gambo Isa wanda kantoman riƙon ƙwarya ne a ƙaramar hukumar Garko.

Sauran mutane 19 da ake gudanar da bincike akan su sune waɗansu masu ajiyar kuɗaɗe da wasu manyan jami’an ƙananan hukumomi mabanbanta.

A na zargin su ne da tura wa juna kuɗaɗe zuwa asusunsu da kuma cire ƙuɗaɗen a wasu lokuta wanda a sakamakon bincike, aka gano miliyoyi daga gare su yayin da har yanzu ake cigaba da bincike game da al’amarin.

Kazalika, an gano cewa miliyan 660 ɗin, wani ɓangare ne na Naira biliyan 1.1 da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya ware don ayyukan samar da ruwa da magunguna.

By Babaji