Tinubu zai rantsar da sabuwar Alƙalin Alƙalan Najeriya ranar Juma’a

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A ranar Juma’a ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar Alƙalin Alƙalan Najeriya.

Mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Za a gudanar da bikin rantsuwar ne a zauren Majalisar Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kekere-Ekun za ta gaji Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a kujerar bayan da ya kai shekaru 70 da haihuwa wanda hakan ke nuna lokacin murabus ɗinsa daga aiki.

Tinubu ya kuma taya Ariwoola murnar kammala aikinsa lafiya tare da jinjina masa ga hidimar da ya yi wa ƙasa.

By Babaji