Olukayode Ariwoola ya yi ritayar aiki a matsayin Alƙalin Alƙalai na Nijeriya

Spread the love

Mai shari’a Olukayode Ariwoola yayi ritaya daga matsayin Alƙalin Alƙalai na Nijeriya. Ariwoola wanda aka haifa a shekarar 1954, yayi ritaya bayan cika shekara 70 na haihuwa kuma shine alƙalin alƙalai na 122 a Nijeriya.

An shirya wa Ariwoola wata ƙaramar liyafa a harabar babbar kotun ƙasa a ranar Alhamis 21 ga Agusta 2024.

A lokacin da yake magana, Ariwoola yayi kira da a ɗauki matakai muhimmai waɗanda za su ragewa babbar kotu matsin aiki.

Ya bayyana cewa akwai shari’a da dama da ke gaban kotun wanda ya kamata ace an gama su a kotun ɗaukaka ƙara.

Ya cigaba da cewa, adalci na yiyuwa ne in har masu shari’a ba za su jira na tsawon lokaci ba domin su san matsayar su.

By ukarofi