Ana cigaba da alhinin mutuwar Sarkin Gobir na Sabon Birni

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

A Nijeriya, al’umma na cigaba da alhinin kashe Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Isa Bawa, wanda ya rasa ransa a hannun ‘yan bindiga bayan sun nemi a biyan kuɗin fansa.

Rahotanni da dama suka fita a ranar Laraba, sun bayyana cewa, ‘yan ta’addar ne suka kashe shi bayan ba a kai mu su kuɗin da suka nema ba.

Da farko dai ba a tabbatar da rasuwar Sarkin ba sai bayan zurfin bincike da aka gudanar wanda a sakamakon haka ne gidajen jaridu suka yi ta ruwaitowa ciki har da BBC inda al’ummar Gobir suka shiga alhini rashin.

Garkuwa da kuma kisan Sarkin sun haifar da ƙarin damuwa a yankin Arewa game da ayyukan ta’addanci da rashin tsaro wanda hakan ya ƙara sanya ƙoƙarin hukumomi na daƙile ayyukan ‘yan ta’adda cikin babban ƙalubale.

Kawo yanzu dai babu wani jawabi daga hukumomi game da batun kisan Sarkin.

Al’ummar Gobir na ci gaba da jimami da alhinin mutuwar Sarkin nasu yayin da ƙasa ta shiga ɗimuwa kan tasirin abin alhinin.

Sai dai ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayin da aka kashe, Hon. Shuaibu Gwanda Gobir ya ce rashin kai kuɗin fansa wa ‘yan bindiga daga gwamnatin jihar Sakkwato ya sa mahaifinsa ya rasa ransa.

Makonni uku da suka gabata ne ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da Sarkin mai suna Alhaji Isa Muhammad Bawa tare da ɗaya daga cikin ‘ya’yansa inda suka buƙaci a bada miliyan N60 wanda a ciki suka ce a saya mu su babur guda biyar.

An kashe Sarkin ne a ranar Talata, 20 ga watan Agusta, kwana ɗaya bayan sako wani bidiyo da ‘yan bindigar suka yi na dukan sa da su ke yi.

Bayan sako bidiyon ne sai Hon. Gwanda a wata hira da manema labarai ya ce sun yanke shawarar haɗa kuɗin a tsakaninsa da sauran mambobin ahalin gidan Sarkin, sai suka samu labarin cewa gwamnatin jihar ta ce za ta biya a ranar Litinin.

A ranar ne kuma suka ji labarin an fitar da kuɗin inda ya ce suka buƙaci gwamnatin ta kai ma ‘yan bindigar tunda ta na tattaunawa da su.

Daga nan ne sai suka samu labarin Sarkin ya rasu a washe gari ba tare da samun rahoton kai kuɗin fansar ba.

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya yi alla-wadai da kisan Sarkin, kuma ya sha alwashin ɗaukar matakan magance matsalar tsaro a ƙasar.

Shugaban ya yi wannan ta’aziyya ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labaru, Ajuri Ngelale.

Sanarwar ta ce: “Shugaba Bola Tinubu ya yi alla-wadai da abubuwan da suka faru waɗanda suka kai ga kisan Sarki Alhaji Isa Bawa.

Shugaban ya kuma bayyana cewa wajibi ne a hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.

ɓangaren sojoji kuwa, Babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da kamo waɗanda ake zargi.

Cikin wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta, an ga yadda wasu da aka yi zargin sojoji ne sun kashe mutum uku tare da shanu aƙalla 100 a kasuwar Sabon Birni da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi a jhar Kaduna.

To sai dai cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya ta fitar ta hannun daraktan yaɗa labaranta, Onyema Nwachukwu, ta jajanta wa iyalan al’ummar yankin Sabon Birni da mutanen da lamarin ya shafa, tare da alƙawarta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

”Kuma duk jami’in da muka samu da hannu a wannan lamarin, to za mu ɗauki matakin da ya dace a kansa,” kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Sanarwar ta ci gaba da cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ɗora wa rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, don haka ba za ta lamunci duk wani yunƙurin saɓanin hakan ba.

By ukarofi