Ku kare kawunanku da kanku – Gwamnatin Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ta yi kira ga al’ummar jihar akan su tashi tsaye don su kare kansu daga hare-haren ɓarayin daji waɗanda ke ci gaba da addabar wasu ƙananan hukumonin jihar.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida Na Jihar, Dakta Nasir Mu’azu ɗanmusa, ne ya yi wannan kira lokacin da yake ganawa da manema labarai a babban birnin jihar.

Kwamishinan ya nuna damuwarsu game da yadda al’umma ke fargabar fito na fito da ‘yan ta’addan duk da cewa sun fi ‘yan bindigar yawan makamai.

A cewar ɗanmusa, ‘yan bindigar da ke addabar ƙaramar hukumar Batsari bindigogin da suke da su basu wuce guda 34 ba, a yayin da al’umar ƙaramar hukumar ke da bindigogi aƙalla 800. 

“A yankin Batsari kawai, akwai jami’an tsaro da jami’an tsaro na al’umma, akwai kuma ‘yan sa kai da ɗaiɗaikun mutane da ke da bindigogi,” inji shi.

Kwamishinan ya ce, matsalar tsaro a jihar ta faru ne a dalilin harkokin noma wanda shine ke bai wa ‘yan ta’adda damar gudanar da harkokinsu na ta’addanci.

Kazalika, cikin watan Fabrairu, 2024 gwamnan jihar Dikko Umar Raɗɗa shi ma ya yi irin wannan kiran ga al’ummar jihar a lokacin da ya jagoranci wani zaman tattaunawa tare da jami’an tsaro, jami’an gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki a harkar tsaron jihar.

A cewar gwamna Raɗɗa, bai kamata al’umma su naɗe hannu suna jiran sai gwamnati ta kare su daga hare-haren ‘yan bindigar.

“Gwamnatin jihar Katsina a shirya take don ta taimaki al’ummar jihar da dukkan abinda suke buƙata don su kare yankunansu,” inji gwamnan.

By ukarofi