Cin hanci da rashawa babban dodo ne da ke neman haɗiye ƙasar nan – Hukumar ICPC 

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Shugaban Hukumar Hana Almubazzaranci da Dukiyoyin Al’ummar da Sauran Laifuka ta ƙasa (ICPC) Dr Musa Adamu Aliyu ya shawarci ‘yan jarida da ke Kano da su jajirce su kuma maida hankali wajen yin rahotanni da za su bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

Musa Aliyu ya bayyana haka ne a yayin wani horo na yini guda da aka shiryawa ‘yan jaridun da ke yaɗa labarai ta yanar gizo a ƙarƙashin ƙungiyar ASKOJ a ranar Laraba a Kano.

Ya kuma yi kira ga ‘yan jarida da su zama a faɗake wajen bada labarin abubuwan ci gaba da za su ɗaukaka martabar ƙasar a duniya, maimakon bayar da rahoton ayyukan tada ƙayar baya da sauran abubuwan da ba su dace ba.

Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin mataimakin kwamishinan ICPC Hassan Salihu, ya ce hukumar ta ga ya zama dole ta haɗa kai da ‘yan jaridun yanar gizo domin su san abubuwan da ake buƙata na bayar da rahoton ayyukan ICPC .

Shi ma a nasa jawabi, Kwamishin ICPC na Kano Barista Ibrahim Abubakar Kagara, da ya samu wakilcin Abubakar Jibrin  ya ce maƙasudin gayyato ‘yan jarida na yanar gizo, shi ne domin kawo ƙarshen babban dodo dake neman haɗiye ƙasar nan wato cin hanci da ba rashawa.

Ya ƙara da cewa “Kafin wannan mun yi wa kafafen yaɗa labarai na da aka saba da su wato na Radiyo da Tɓ, yanzu shi ne muka ga ya dace mu shirya wa ‘yan jarida na zamani wato na online, domin a samu kusanci mu daku ya ta yadda za mu yi aiki tare don yaɗa abinda ke faruwa a fagen yaƙi da rashawa a haƙiƙanin yadda yake, bai aita ruruta al’amura ba.

A jawabinsa shugaban ƙungiyar ‘yan jaridu yanar gizo Yakubu Salisu ya yaba wa hukumar ta ICPC bisa shirya wannan bita ta kwana ɗaya ga ‘yan jaridun dake aiki a yanar gizo.

Ya bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne a shekarar 2020 da nufin haɗa kan ‘yan jaridan domin cimma manufofin da aka sa gaba.

Yakubu Salisu ya buƙaci mahalarta taron da su yi amfani da damar da suka samu domin bunƙasa aikinsu a yaɗa labarai.

Kazalika a yayin horon, an gabatar da kasidu daban-daban da suka shafi aikin hukumar.

Taron dai ya samu halartar masu jaridun yanar gizo daban-daban da ke faɗin jihar Kano.

By ukarofi