‘Yan bindiga sun kashe manoma 13 a Jihar Neja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan bindiga sun kashe mutane 13 a gonakinsu a yankin Ijuwa na yankin Alawa na ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Shugaban ƙaramar Hukumar, Akilu Isyaku, ya tabbatar da kashe manoman 13 a wata hira da ya yi da wani gidan rediyo a Minna ranar Laraba.

Ya ce ‘yan bindigar sun harbe tara daga cikin wadɗanda abin ya shafa har lahira, yayin da aka kashe wasu huɗu a wani wuri daban a rana guda.

Wani ɗan yankin da ya zanta da News Point Nigeria ya kuma ce ‘yan bindigar sun auna al’umma ne a kan zargin cewa mambobinsu na bai wa jami’an tsaro bayanan sirri kan duk wani motsi na ‘yan bindigar.

A halin da ake ciki, muƙaddashin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba ya bayyana harin a matsayin na shaidan da kuma rashin tausayi.

Garba a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya jajentawa iyalai da al’ummar ƙaramar hukumar Shiroro da sauran al’ummar da abin ya shafa.

Wannan harin ya faru ne a lokacin da ake sa ran manoman za su yi ƙarin lokaci a gonakinsu. An tattaro cewa wasu manoma da dama da ke nesa da inda harin ya faru sun bar gonakinsu saboda fargabar harin.

By ukarofi