Al’ummar gari sun kama mai garkuwa da mutane a Filato

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Al’ummar yankin Nepa da ke garin Jos sun yi kukan kura sun kama mai garkuwa da mutanen ne a ranar Alhamis, suka miƙa shi ga ’yan banga.

Wani ɗan banga a yankin da ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce ’yan banga sun miƙa wanda ake zargin ga ofishin ’yan sanda na Laranto.

Dan bangan ya ce wanda ake zargin, “ya yi garkuwa ne da wasu ƙananan yara biyu, ya karɓi kuɗin fansa Naira miliyan 1.5 daga iyayensu, amma ya ci gaba da riƙe yaran.

 “Washegari da ya je wani kango da ya ɓoye yaran ne mutanen da ke wucewa a wurin suka ji kukan yara, shi ne suka shiga ciki.

“Da shigarsu sai wanda ake zargin ya haura taga ya tsere, suka bi shi suka yi masa ihu, mutane suka fito maza da mata aka kama shi.

“Daga nan suka miƙa shi a hannun ’yan banga, su kuma suka kai shi ofishin ‘yan sanda na Laranto tare da tsabar kuɗi N1,492,000 da ya riga ya karɓa daga iyayen yaran.”

Kakakin ’yan sanda na Jihar Filato, DSP Alabor Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun rundundar tana gudanar da bincike a kansa.

By ukarofi