Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili ta yi zargin cewa fadar shugaban ƙasa da majalisar dokokin ƙasar sun yanke shawarar zama ‘yan fashi da makami a Nijeriya.
Daily Trust ta rawaito cewa Ezekwesili ta bayyana hakan ne a lokacin da take tsokaci kan siyan sabon jirgin shugaban ƙasa, yayin wata tattaunawa da ta yi da gidan talabijin na Channels Tɓ’s Politics Today.
Ta ce an sayi jirgin a yayin da ‘yan Nijeriya na shiga ƙara shigewa cikin ƙangin talauci duk minti ɗaya.
Ezekwesili ta ce, “A duk abin da muka ji, suna cewa wai tsohon jirgin shekararsa 19, wato su na ƙoƙarin bada hujjar sayan sabon jirgin.
“Raina mana hankali kawai su ke yi. Hukumomin zartaswa, fadar shugaban ƙasa, Majalisar Dokoki ta ƙasa, ina ganin sun yanke shawarar cewa su ne ‘yan fashi ne ga talakawan Nijeriya.
“Yan siyasa sun yanke shawarar cewa su ‘yan fashi ne a kan ‘yan Nijeriya. Domin ban ga yadda zai yiwu a ce fifikon gwamnatin da ke da irin wannan matsananciyar yunwa a cikin ƙasa ba, irin wannan talauci da mutane ke fadawa cikin sa a duk minti daya bai kamata a yi tunanin ma sayen jirgin sama ga shugaban ƙasa.
“Ginawa mataimakin shugaban ƙasa gida na Naira biliyan 20; siyan motoci iri-iri, wasu ma masu ban dariya da kuma motocin yan majalisar tarayya da na zartaswa, menene ainihin hikimar wannan?”
Ta ƙara da cewa babu wanda zai tausayawa Tinubu domin ya ɗora akan duk wasu manufofi da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi.
