Barcelona ta saka ’yan wasa uku masu shekara 17 a tare a La Liga

Spread the love

Barcelona ta fara kakar 2023/24 da kafar dama, bayan da ta je ta doke ɓalencia 2-1 ranar Asabar a wasan makon farko a La Liga.

To sai dai ƙungiyar ta yi amfani da matasa uku masu shekara 17 a karawar da ta je ta ci ɓalencia.

Cikinsu sun haɗa da Lamine Yamal da Cubarsi da kuma Marc Bernal, waɗanda aka fara fafatawar da su.

Karo na biyu da Barcelona ta yi amfani da ’yan ƙwallo uku a lokaci ɗaya masu kasa da shekara 18.

Haka kuma Barcelona ce keda wannan tarihin a karni na 21 ta kuma kara maimaita hakan a bana.

Ta fara yin hakan a Mayun 2024 lokacin da ɗaɓi ke koci, wanda ya fara da Lamine Yamal da Cubarsi da kuma Hector Fort a karawa da Almeria.

Hansi Flick shi ne ke horar da Barcelona, bayan da ƙungiyar ta raba gari da ɗaɓi a bara.

Barcelona na fama da matsin tattalin arzikin da take tsuke bakin aljihu, sannan tana ƙoƙarin bin dokar La Liga ta kashe kuɗi daidai samu.

A kakar nan ta bana Barcelona ta sanar da cewar ƙyaftin ɗinta, Sergi Roberto ya bar ƙungiyar.

Haka kuma ta sayar da Marc Guiu ga Chelsea a cikin watan Yuli da kuma Julian Araujo da ya koma Bournemouth cikin watan Agusta.

Ita kuma ta ɗauki Dani Olmo ranar 9 ga watan Agusta daga RB Leipzig.

A kakar da ta wuce Barcelona ta kare a mataki na biyu a teburin La Liga, inda Real Madrid ta lashe kofin tare da na Champions League.

Ranar Asabar Barcelona za ta karɓi baƙuncin Athletic Bilbao a wasan mako na biyu a La Liga.

A ɗaya ɓangaren, Barcelona ƙaraashin sabon koci, Hansi Flick ta fara La Liga ta bana da nasara, bayan da ta je ta ci ɓalencia 2-1 ranar Asabar.

Flick tsohon kocin tawagar Jamus da Bayern Munich ya koma Barcelona ne, bayan da ta sallami ɗaɓi.

ɓalencia ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Hugu Duro, bayan tamaula da ya samu ta wajen Diego Lopez ya buga ta wuce Marc-Andre ter Stegen.

Daga baya ne aka yi bani-in-baka tsakanin Robert Lewandowski da Lamine Yamal da ta kai Lewandowski ya farke ƙwallon.

ɓalencia ta sa kaimi da yawa, amma Barcelona ta nuna cewar da gaske take a bana, inda ta yi ta sa ƙwazo a karawar.

Daga baya ne Lewandowski ya ƙara na biyu a bugun fenariti, bayan da aka yi wa Raphinha ƙeta.

Yamal ya gagari ɓalencia, inda mai shekara 17 ya dunga warwasa tamaula son ransa da ya dunga zama baraza na ga masu masauƙin baki.

Haka dai Barcelona ta ci gaba da wasan har zuwa ƙarshensa, inda ta tsira da maki uku da ƙwallo biyu a raga aka zura mata ɗaya a wasan farko a La Liga ta 2024/25.

Barcelona, wadda ta yi ta biyu da tazarar maki 10 tsakaninta da Real Madrid, wadda ta lashe kofn bara za ta fuskanci Athletic Bilbao a wasan mako na biyu ranar Asabar 24 ga watan Agusta.

By ukarofi