Shettima ya umarci sojoji su tsaurara matakan kariya na ƙalubalen tsaro

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya umarci rundunar jami’an sojin Nijeriya da su kasance masu lura da kuma ɗaukar matakan da suka dace wajen tunkarar matsalolin tsaro da ke shiyyoyinsu.

Shettima ya yi kiran ne a lokacin bikin yaye ɗaliban sojoji na Kwalejin Nazarin Tsaro ta Ƙasa (NDC) a Kwas na 32 a Abuja.

Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a taron, ya ce gwamnatinsu na da burin mayar da Nijeriya waje mai tsaro don zuba hannun-jari da samar da nasara ga tattali.

Ya kuma yi tsokaci game da buƙatar shugabanci mai salo na magance rashin tsaro a ƙasar.

Ɗalibai 111 suka yi kwas ɗin tare da wasu ƴan ƙasashen waje guda 19 inda Shettima yayi kira gare su da su zama masu sanin darajar kishin ƙasa.

Ya kuma ce, gwamnati za ta yi nazari game da shawarwari da suka bayar a rahotonsu kuma ta zartar da su, ya na mai yi mu su alƙawarin gwamnati za ta kammala ginin makarantar NDC ta dindindin.

By Babaji