Darakta Janar na Hukumar Leƙen Asiri, Ahmed Abubakar ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda wasu dalilai da suka shafe shi da iyalansa.
Abubakar ya faɗi haka ne bayan miƙa takardar ajiye aiki da yayi a fadar shugaban ƙasa a yammacin Asabar. Ya cigaba da cewa, zuwan na ranar Asabar zuwa ne da a ka saba domin ba shugaban ƙasa bayanai na abubuwan da ke faruwa a kan sha’anin tsaro a ƙasar.
Daga ƙarshe ya godewa Shugaban ƙasa domin ƙara masa wa’adin wata 15 da ya yi domin ya jima a ofis ɗin tun shekarar 2018.
Da ƴan Jarida su ka tambaye shi, ya ce “ba wani dalili ne mai tada hankali ba, dalilai ne da suka shafe ni da iyalai na in ji shi”
Daga ƙarshe ya godewa Shugaban ƙasa da ya bashi wannan damar yin aiki dashi, ya bayyana cewa ba abu ne mai sauƙi ba, yin aiki ƙarkashin shugabannin ƙasa biyu.
Da aka tambaye shi, ya ya shugaban ƙasa ya amshi murabus ɗin na shi, ya ce “shugaban ƙasa ya fahimce shi, kuma ya yi ma shi fatan alheri, duk wani bayani za su ji daga bakin mai ba shugaban ƙasa shawara ta fannin tsaro na ƙasa”
