Gwamnatin Tarayya ta yi ƙarin haske game da kuɗin karatu na kwalejojin haɗin kai

Spread the love

Dage BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ma’aikatar Ilimi ta yi ƙarin haske game da batun rahoton da ke cewa an ƙara kuɗin karatu a makarantun sekandire na gwamnati da aka fi sani da ‘Unity Schools’.

Rahotanni da a ke yaɗawa a wata takarda ta kafofin labarai musamman ta kafar X (Twitter) sun ce sabbin ɗalibai da za su shiga irin makarantun za a buƙaci su biya Naira 300,000 yayin da tsoffin ɗalibai su ma akwai adadin da aka yanke mu su.

Ga takardar a ƙasa👇 kamar yadda za a gani:

Takardar ta haifar da cecekuce wanda hakan ya sa tsohon shugaban hukumar Tabbatar da Ƴancin Ɗan-adam ta Ƙasa (NHRC), Farfesa Chidi Odinkalu ya buƙaci da a sanya kuɗin karatu a makarantun bisa kima.

Saidai ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa ta ƙaryata rahoton da aka fitar a takardar, ta na mai tabbatar da cigaba da bayar da ilimi kyauta ga ɗalibai kamar yadda Daraktar ilimin babban sekandire ta ma’aikatar, Binta Abdulkadir ta faɗa cikin wata sanarwa a ranar Asabar, inda ta ce saƙon da takardar ke ƙunshe da shi damfara ce tsantsa.

Sanarwar ta ce, takardar ba daga hukumar ta ke ba wadda akwai kurakurai da dama da suka ƙunshi adireshin da ba daidai ba da kuma kurakuran rubutu.

Don haka, ma’aikatar tayi watsi da takardar sakamakon ƙoƙarin wautar da mutane da rikita tunanin iyayen yara gami da ruɗar da al’umma.

Bugu da ƙari, sanarwar ta ce mafi girman kuɗin da a ke karɓa a makarantun shine Naira 100,000 kacal wanda ya ƙunshi duk abin da ake bai wa ɗalibi a yayin karatunsa. Saboda haka, ta ke kira ga al’umma su binciki irin makarantun da ke kusa da su don tantancewa.

By Babaji