Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Za a maka Gwamnan Jihar Sakkwato a Kotun Duniya akan kisan gillar da ‘yan bindiga suka yi wa Mai Martaba Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Isa Bawa, bayan garkuwa da shi da suka yi tsawon makonni uku.
Shugaban gamayyar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na Afirka, Hon. Dr Sulaiman Sha’aibu Shinkafi, shi ne ya bayyana hakan cikin makon nan yayin da yake zantawa da manema labarai a Sakkwato.
Dr Sulaiman Shuaibu ya ce gamayyar ƙungiyoyinsu 18 sun yi allawadai da kisan basaraken kana sun ɗauki laifin wannan ta’asa kacokan sun ɗora wa gwamnatin Jihar Sakkwato, domin a cewarsa sune suka yi sakaci da rayuwarsa har abin ya kai ga haka.
Shugaban ƙungiyar ya kuma zayyano wasu buƙatu da ƙungiyar ke son gwamnatin Jihar Sakkwato ta gaggauta aiwatar da su cikin mako biyu, idan ba haka ba a cewarsa ba su da wani zaɓi da ya wuce su maka shi Kotun Duniya ICC domin bi wa iyalan Sarki da al’ummar Gobirawa da Arewa haƙƙinsu.
Buƙatun kuwa sune kamar: ƙungiyar na son gwamnatin Sakkwato ta gaggauta korar kwamishinan tsaron jihar, saboda a cewarta bai san aikinsa, bai kuma iya kiyaye rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Haka kuma ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin Sakkwato da ta biya iyalan Marigayi Sarkin Gobir diyyar rai, saboda a cewarta “sakacin gwamnatin jihar ne”.
Hakazalika sun yi kira ga gwamnatin jihar Sakkwato ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmad Aliyu da ta gaggauta fitar da jawabin manema labarai ga al’ummar Gobirawa, jihar Sakkwato, Arewa da Nijeriya bakiɗaya domin kwantar musu da hankali.
ƙungiyar ta kuma jaddada cewa, ƙin yin hakan zai tilasta musu maka gwamnan jihar a Kotun Duniya.
“Wallahi, wallahi kada a ɗauka wasa mu ke yi, mun ba gwamnatin Sakkwato wa’adin makon biyu ta biya waɗannan buƙatu da muka zayyano, idan ba haka ba ba mu da wani zaɓi sai shigar da ƙara Kotun Duniya,” shugaban ƙungiyar ya jaddada.
