Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙungiyar likitoci da su janye yajin aikin gargaɗi da su ka shiga na kwana bakwai.
Ƙaramin ministan lafiya Tunji Alausa ne ya bayyana haka yayin da ya kai wata ziyara asibitin ido na ƙasa da ke Kaduna.
In ji ministan, yanzu haka tattaunawa na gudana da waɗanda su kai garkuwa da Dr Ganiyat Popoola domin ganin sun sake ta cikin aminci. Ya bada tabbacin duka jami’an tsaro suna bakin ƙoƙarin su tare da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribado domin ganin an sake ta cikin aminci.
Ministan ya cigaba da bayyana yadda masu garkuwa da ita su kai ta canza buƙatun su na fansar ta amma ya ce duk da wannan za su cigaba da aiki domin ganin an ceto Dr Ganiyat Popoola.
Abun farin ciki shine, sun tabbatar har yanzu ta na nan da ranta don haka za su cigaba da duk abinda yakamata domin ganin ta samu ƴanci.
