Ƙungiyar Afenifere ta nemi gwamnati ta bar ƴan hidimar ƙasa su yi aiki a shiyyoyinsu

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wata ƙungiyar al’ummar Yarbawan Nijeriya mai suna Afenifere tayi kira ga gwamnatin tarayya ta bai wa ɗalibai masu hidimar ƙasa na NYSC izinin yin ayyukansu a shiyyoyinsu.

Hakan na zuwa ne sakamakon ƙara ƙamari da ayyukan garkuwa da mutane da ta’addanci suka yi yawa a Nijeriya.

Afenifere ta yaba wa gwamnatin da hukumomin tsaro kan ceto ƴan hidimar ƙasa da aka yi garkuwa da su akan hanyarsu daga jihar Akwa-Ibom zuwa Sakkwato.

Ƙungiyar ta jaddada buƙatar inganta jami’an tsaro don su ƙara haɓaka ƙoƙarinsu na kawo ƙarshen waɗannan ƙalubalen da al’ummar ƙasa ke fuskanta.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, Mista Jare Ajayi ya fitar, ƙungiyar ta ce hakan zai taimaka wajen rage yawaitar zirga-zirga zuwa mabanbanta sassan Nijeriya la’akari da halin da harkar tsaro ke ciki.

Ya ƙara da cewa, akwai buƙatar gwamnati ta yi ƙoƙarin shawo kan matsalar taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar, ya na mai cewa a yi la’akari da mambobin NYSC ta hanyar ba su damar yin hidima a kusa da gidajensu.

By Babaji