
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da ƙarar da aka shigar don hana zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya sakamakon rashin bayyana daga ɓangaren waɗanda suka shigar da ƙarar.
A ranar Alhamis ne Mai Shari’a Peter Lifu ya yi hukuncin bayan rashin bayyanar ƴan ɓangaren kai ƙarar mutum 17 a kotun inda suka bar mutane 26 da ke kare ƙara a kotun ba tare da wata gabatarwa a hukumance ba.
Masu ƙarar, waɗanda sun zo ne daga shiyyoyi shida na ƙasar nan sun shigar da ƙarar ne inda suka nemi kotun ta ɗauki mataki akan zanga-zangar wadda a cewarsu, zata daƙile ƴancin zirga-zirgar al’umma, mutuncin ɗan-Adam, mallakar kadarori da zaman lafiya da tsaron ƙasa baki ɗaya.
Sun nemi kuton ta umarci hukumomin tsaro da su ɗauki mataki kan masu zanga-zangar inda suka bayar da misali da irin damejin da zanga-zanga ta haifar a jihohin Kano, Kaduna da Jigawa ga kadarorin gwamnati da na al’umma.
Waɗanda ke kare ƙarar sune; Omoyele Sowore, Antoni Janar na Ƙasa, Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Sufeto Janar na ƴan sanda, shugaban rundunar sojojin ƙasa, shugaban ma’aikatan tsaro da sauran su.A sakamakon rashin bayyanarsu da kuma rashin wakilci a hukumance ya sanya alƙalin ya yi watsi da ƙarar.
Kazalika, ƙara tana da alaƙa da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta da wasu matasa suka jagoranta sakamakon rashin gamsuwa da yadda halin tattalin arziƙin ƙasa ke ciki.
