



Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa ayyukan tituna da ake gudanarwa a faɗin jihar na ɗaya daga cikin dalilan da ke nuna ƙoƙarinsa wajen bunƙasa harkar sufuri wa al’ummarsa.
A ranar Laraba ne gwamnan ya ƙaddamar da buɗe aikin tituna masu tsawon kilomita 11.65 da zasu haɗe garuruwan Rawayya, Furfuri, da Kurya Madaro a ƙananan hukumomin Bungudu da Ƙauran Namoda.
Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce an bai wa kamfanin ‘Bauhaus Global Investment Nigeria Limited’ ne aikin akan tsabar kuɗi da adadinsa ya kai Naira biliyan 6.6 wanda ake fatan kammala shi cikin shekara ɗaya.
Dauda Lawal ya ce, banbanci mai rata da yawa da ake samu tsakanin ababen more rayuwa da ke tsakanin birane da ƙauyuka su suka haifar da cikas ga ci gaban jihar, ya na mai cewa hakan na shafar manoma da kuma masu ƙananan sana’o’i.
Ya ƙara da cewa, aikin zai taimaka wajen haɗe birane da ƙauyuka ta yadda za a samu sauƙin sufuri tsakanin al’ummar yankunan don gudanar da harkokinsu cikin walwala.
Kazalika, gwamnan ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa, gwamnatinsa zata cigaba da ƙoƙarin samar da ababen more rayuwa gare su ta hanyar samar da ci gaba a baki ɗaya sassan jihar.
