
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero ya dawo hedikwatar ƙungiyar bayan amsa gayyatar da rundunar ƴan sanda ta yi masa a kwanakin baya.
A safiyar ranar Alhamis ne Ajaero da lauyan kare ƴancin Ɗan-adam, Femi Falana tare da wasu mutane suka raka shi zuwa ofishin rundunar da ke Abuja.
An gayyace shi ne sakamakon wani bincike da ƴan sanda ke gudanarwa na zargin ɗaukar nauyin ta’addanci wanda hakan ya kai ga ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka fara zargin gwamnatin tarayya da ƙoƙarin cin mutuncin shugabannin ƙwadago.
Gabannin amsa gayyatar, shugabannin ƙwadago sun shirya yin tattaki tare da mambobinsu zuwa kowace babbar ofishin rundunar ƴan sanda da ke jihohi 36 a Nijeriya.
Jami’an ƴan sun ce ana zargin Ajaero ne da hannu a laifukan ɗaukar nauyin ta’addanci da sata ta yanar gizo da zamba cikin aminci da makamantansu.
