Gwambatin Tinubu ta amince da tallafin lantarki na kashi 50 ga asibitoci

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙaramin Ministan Lafiya da Kula da Al’umma, Dakta Tunji Alausa ya ce gwamnatin tarayya ta amince da kaso 50 na tallafin wutar lantarki ga asibitoci a faɗin Nijeriya.

Ya ce, gwamnatin ta yi hukuncin ne domin rage tsadar kiwon lafiya a asibitocin da kuma tasirin sa marasa lafiya.

A lokacin ƙaddamar da tashar lantarki na ‘solar’ a asibitin marasa lafiyar ƙwaƙwalwa na Barnawa da ke jihar Kaduna, Ministan ya ce za a sauya sunayen asibitocin gwamnati zuwa ‘Specialist’ ta yadda za su faɗaɗa ayyukansa ga kula da sauran nau’ukan marasa lafiya.

Ya kuma jinjina wa Daraktar Lafiya ta asibitin, Dakta A’ishatu Yusha’u Armaya’u kan nasarorin da asibitin ke samu wanda hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin cika alƙawarin Shugaba Bola Tinubu a lokacin da ya ke yawon neman zaɓe.

By Babaji