
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wasu masu datsa a yanar gizo sun datsi shafin facebook na hukumar Hisba ta Kano inda su ke saka ababen da suka shafi batsa wanda hakan ya haifar da cecekuce.
Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar da faruwa al’amarin inda ya ce su na ƙoƙarin shawo kan matsalar wacce tsawon kwana uku kenan da farawarta.
Ya ce, ɓangaren harkar yanar gizo na hukumar na cigaba da ƙoƙari wajen ganin shafin ya dawo aiki yadda aka saba.
Ya kuma yi kira ga al’umma su taimaka wajen ganin an samu gyarar ta hanyar aika rahoto ga Meta wanda yayi alƙawarin warware matsalar nan da kwana biyu.
Shugaban ɓangaren harkar yanar gizo na hukumar, Sani Zailani, yace wannan ba shi ne karo na farko da ake kai hari ga shafin ba inda a baya ma an sha samun irin haka.
