
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Yunƙurin ficewa daga Napoli zuwa Chelsea na Victor Osimhen ya samu cikas yayin da aka rufe kasuwar hada-hadar ƴan wasa.
Hakan na zuwa ne bayan da ƙungiyoyin biyu suka gaza cimma matsaya game da ɗan wasan.
Haka zalika, zuwansa ƙungiyar Al-Ahli ta ƙasar Saudiyya zai yi wuya bayan da ta sayi Ivan Toni na Brentford a ranar da aka rufe hada-hadar.
Don haka, Osimhen zai cigaba da zama a Napoli a halin tsaka mai wuya saboda ƙungiyar ta sayi Rumelu Lukaku inda ta ɗauki lambar ɗan Nijeriyan ta bai wa sabon ɗan wasan.
Rahotonni sun bayyana cewa, a halin yanzu, Napoli ta cire sunan Osimhen daga cikin jadawalin ƴan wasanta da za su ke fafatawa a fagen fama da abokanan karawa.
