Napoli ta cire Osimhen daga cikin ƴan wasanta na Serie A, ta bai wa Lukaku lamba 9

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli ta cire Victor Osimhen acikin jadawalin ƴan wasanta da ke fafatawa a gasar Serie A ta ƙasar Italiya bayan samun tseko da aka yi a ƙoƙarin ficerwarsa daga ƙungiyar.

Ƙungiyoyin Chelsea da Al-Ahli ta ƙasar Saudiyya ne suka so sayen sa wanda hakan bai yiwu ba sakamakon rufe kasuwar hada-hadar ƴan wasa da aka yi a jiya.

Tuni dai Napoli ta sayi ɗan wasa Rumelu Lukaku don ya maye gurbin Osimhen da tunanin zai koma Chelsea.

A yanzu haka dai Osimhen na halin tsaka mai wuya sakamakon jefar da shi da ƙungiyar tasa ta yi daga cikin waɗanda za ta tafi da su a kakar wasa ta bana.

By Babaji