Kotu ta yi watsi da tuhumar ƴan zanga-zanga

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Babbar kotu a Abuja ta yi watsi da ƙarar tuhumar da aka shigar kan masu zanga-zangar matsin rayuwa.

Mutane 17 ne suka shigar da ƙarar inda su ke ƙalubalantar zanga-zangar gama gari da aka gabatar wacce kotun ta yi watsi da ita kasancewar ba a gabatar da waɗanda ake tuhuma ba akan lokaci.

Mai Shari’a Peter Lifu yayi hukuncin kasancewar masu ƙarar mutum 17 da 26 da ke kare ta ba su bayyana ba a kotun kuma ba tare aikawa da wakilci ba a hukumance.

Masu kare ƙarar sun haɗa da; ƴan ƙungiyar ‘Take it Back’, ‘Nigerians against humger’, jami’an DSS, Sufeton ƴan sanda, rundunar sojoji da kuma shugaban hedikwatar tsaro.

A sakamakon rashin bayyanarsu ne Alƙalin ya bayyana rashin damuwarsu da cigaba da sauraron ƙarar a matsayin dalilin yin watsi da ita.

By Babaji