Gwamnan Zamfara ya ziyarci waɗanda ambaliya ta rutsa da su tare da ba su tallafi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A ranar Asabar ne gwamanan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kai ziyarar gani-da-ido a yankunan da ambaliya ta afka mu su a ƙaramar hukumar Gummi da ke jihar.

Mamakon ruwan sama da aka yi a satin da ya gabata ne yayi sanadiyyar ambaliya a wasu garuruwa na ƙaramar hukumar wacce ta salwantar da gidaje da dama.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce gwamnan ya fara ne da ziyaratar Fadar Mai martaba Sarkin Gummi, Mai Shari’a Lawal Hassan inda daga nan sai ya garzaya cikin gari domin jajentawa ga waɗanda al’amarin ya shafa.

Baya ga haka ne sai ya tafi garin Gayari don ya ga matakin damejin da ambaliyar ta yi, ya na mai tausayawa tare da cewa tuni tawagar injiniyoyi suka gudanar da nazari kan yankunan don samar mu su da mafita.

“Nan da nan bayan samun labarin aukuwar mummunan lamarin, na aika da kwamishinonina guda biyu don su kai ziyara tare da jajentawa yankunan da abin ya shafa.”

Ya kuma bada tallafin buhunan abinci guda 10,000 da suka haɗa da shinkafa, masara da gero don a raba wa mutanen.

Kazalika, ya ce a madadin gwamnatin Zamfara ya ware tallafin Naira miliyan 100 ga waɗanda lamarin ya rutsa da su tare bai wa kowannen su fili a yankin da babu barazanar ambaliya.

By Babaji