IPC ta caccaki gwamnatin Kano kan tsare ɗan jarida bisa tuhumar ɓata suna

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Cibiyar labarai ta ƙasa-da-ƙasa (IPC) reshen jihar Legas, a ɓangarenta na kula da bada kariya ga ƴan jarida (SPJ) tayi matuƙar nuna damuwarta kan tura wani ɗan jarida da ke aiki da Pyramid a jihar Kano Muktar Ɗahiru zuwa gidan yari.

An kama Ɗahiru tare da tsare shi ne sakamakon yaɗa bayanai da gwamnatin jihar ta bayyana su a matsayin laifi.

SPJ yace, ƴan sanda sun kama ɗan jaridar ne a ranar 29 ga watan Agusta, 2024 kan yaɗa wani saƙo a shafinsa na Facebook.

Rahoton da aka samu daga SPJ ya nuna cewa, an kai shi gidan yarin ne saboda yaɗa saƙo da ke ɗauke da suka ga jami’an gwamnatin jihar ciki har da gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma Mai martaba Sarki Sanusi Lamiɗo Sanusi.

Wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun mai magana da yawun IPC, Melody Akinjiyan, tace Daraktan IPC, Mista Lanre Arogundade ya yi alla-wadai da hukuncin, ya na mai cewa hakan tozarta shugabanci ne.

Ya ce, ya kamata ace an bada belin ɗan jaridar kafin a kai ga zuwa gidan yarin, ya na mai cewa an hukunta shi ne ba tare da ƙwararan dalilai ba.

By Babaji