Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya na shirin zuba jari na zunzurutun kuɗi Dala Biliyan 4.8 a fannin kiwon lafiya a faɗin ƙasar.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yayin da yake ƙarin haske kan sauye-sauyen da gwamnatin ta yi a fannin kiwon lafiya wanda a cewarsa, zai lashe sama da dala biliyan 4.8 wajen zuba jari duk a yunƙurin gwamnati na ganin an farfaɗo da ingancin kiwon lafiya a Nijeriya tare da magance Ƙalubalen da ya jima yana addabar ɓangaren kiwon lafiyar.
Shettima ya bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da rukunin asibitocin Sahad a birnin Abuja.
“Gwamnatinmu ta kuma ƙaddamar da gyare-gyare a kan ɓangarori huɗu masu mahimmanci wanda suka haɗa: sauya tsarin kula da kiwon lafiya, samar da ingatattun ɓangarorin binciken lafiya, buɗe sabbin cibiyoyin , da ƙarfafa sashin riga-kafi ga kamuwa da cututtuka.
Shettima ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su shigo wannan tsarin saboda muhimmancinsu ga cimma burin samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya a Nijeriya.
Kashim ya kuma yaba wa mammallakin Kamfanin Sahad Group of Companies, Alhaji Ibrahim Mijinyawa, bisa namijin ƙoƙarin da yake yi na samar da ingantaccen kiwon lafiya.
Asibitocin Sahad din dai sun ƙunshi ɗakuna masu gadaje 200 da kuma kayan aikin kula da lafiya na zamani.
