
Daga BELLO A. BABAJI
Sama da mutane 10,000 ne ambaliya ta tarwatsa tare da salwantar da dukiyoyin miliyoyin nairori sakamakon ruwan sama da aka yi a makonni kaɗan da suka gabata, a ƙaramar hukumar Gummi da ke jihar Zamfara.
Sarkin Gummi, Mai Shari’a Hassan Lawal (rtd) ya faɗi hakan a ranar Asabar a lokacin da gwamnan jihar, Dauda Lawal ya kai ziyarar gani-da-ido ƙaramar hukumar.
Gwamnan ya ziyarci garuruwan Gummi da Gayari don ganin matakin damejin da ambaliyar ta haifar.
A lokacin da ya ke ganawa da gwamnan, Sarkin ya bayyana yadda ta kasance a ƙaramar hukumar inda ya ce aƙalla magidanta 10,291 ne lamarin ya afka mu su.
A nasa ɓangaren, gwamnan ya bada tallafin buhunan abinci guda 10,000 da kuma Naira miliyan 100 don a raba wa waɗanda lamarin ya shafa.
Ya kuma ce za su yi ƙoƙarin warware matsalolin da ke haddasa ambaliya ta hanyar gina sabbin magudanan ruwa, gyara madatsun ruwa da kuma gina waɗansu.
